Connect with us

SIYASA

APC Ta Shirya Zaben Fid Da Gwani kan Sulhu A Kebbi

Published

on

A jiya ne jam’iyyar APC reshin jihar kebbi ta shirya gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar sulhu a dukkan kujerun da ake neman takara a kansu a jihar, amma ba da kujerar shugaban kasa da kuma ta Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar ba .
Domin dukkan masu ruwa da tsaki da kuma mambobin jam’iyyar na jihar ta kebbi sun yi matsaya guda cewa sun tsayar da Shugaban Muhammadu Buhari da Gwamna Bagudu karo na biyu ga mulkin kasa nan da kuma jihar kebbi a zaben 2019 mai zuwa.
Sanawar shirin gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar sulhu ta fito ne daga bakin shugaban jam’iyyar APC na jihar ta kebbi, Alhaji Bala Sani Kangiwa bayan kammala taron tattaunawa da mambobin jam’iyyar suka gudanar a jiya wanda taron na masu ruwa da tsaki kan harakokin siyasar APC a jihar ta kebbi , domin tattaunawa kan cim ma matsaya ta yadda jam’iyyar za ta gudanar da zaben fid da gwani da za ta soma duk fadin kasar nan a cikin ‘yan kwanakin masu zuwa, don tunkarar zaben 2019 mai zuwa.
An dai gudanar da taron tattaunawar ne a dakin gudanar da taron na fadar gwamnatin jihar ta kebbi da ke a Birnin-Kebbi a jiya.
Shugaban ya bayyana hakan ne yayin wata zantawa da manema Labaru a fadar gwamnatin jihar jin kadan bayan kammala taron tattaunawar na masu ruwa da tsaki a Birnin- Kebbi . Inda ya sheda wa manema Labaru cewa” kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar ta amince da ta gudanar da zaben fid da gwani kan sulhu, idon kuwa sulhun bai samu ba sannan a yi amfani da wakilan mazabu wato (delegate) domin zaben wadanda za su faskanci sauran jam’iyyu a zaben 2019 mai zuwa”. Ya kuma ci gaba da cewa idon kuma an cim ma matsaya ga sulhu ba sai an yi zaben delegate ba.
Kazalika ya kara da cewa “ dokar jam’iyyar ta tsarin gudanar da zaben fid da gwani ga masu neman tsayawa takara ya kasu kashe uku ne kuma shi ne kamar gudanar da zaben ‘yar tinke , zaben delegate ko kuma sulhu a tsakanin masu neman tsayawa takarar kujeru daban-daban, wannan tsarin guda ukun nan shi ne abin da kundin dokar jam’iyyar APC ya tanadas”. Saboda hakan a matakin jiha za mu yi sulhu inda kuma sulhun bai samu ba sannan za mu gudanar da zaben delegate.
Bugu da kari ya ce” A jihar Kebbi mambobin jam’iyyar APC uwa daya uba daya ake , ma’ana babu wata matsala kuma akwai zaman lafiya a tsakanin ‘yan jam’iyyar wanda hakan ne yasan mambobin suka amince da cewa a yi sulhu a tsakanin junna domin suna ganin cewa zai kawo mafita mai sauki ga jam’iyyar da kuma mambobin ta.
Daga karshe ya yi amfani da damar gudanar da taron tattaunawar na masu ruwa da tsaki a jihar ta kebbi domin bayyana wa magoya bayan jam’iyyar APC a jihar cewa ga matsayar da mambobin jam’iyya suka amince da ita. Ya kuma yi kira ga sauran jama’ar jihar da su ci gaba da bai wa jam’iyyar ta APC goyon bayan musumman ga manufufin ta da kuma zabubukan da za a gudanar a shekara ta 2019 mai zuwa. Domin zaben ‘yan takarar da jam’iyyar ta tsayar.
Mahalar ta taron sun hada da tsohon Gwamnan jihar, Sanata Muhammadu Adamu Aliero da Sanata Bala Ibn Na’Allah da Sanata Yahaya Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Alhaji Saidu Usman Dakingari da tsohon ministan Ayyukkan cikin gida Sama’ila Balarabe Sambawa da tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kebbi Alhaji Ibrahim Khali Aliyu da kuma Gwamnan jihar Abubakar Atiku Bagudu.
Sauran sun hada da mataimakin Gwamnan jihar Kanal mai ritaya Sama’ila Yombe Dabai, Shugaban jam’iyyar APC na jihar ta Kebbi Alhaji Bala Sani Kangiwa tare mukaraban san a jaha, shuwagabannin kananan hukumomin, shuwagabannin jam’iyya na kananan hukumomin ashirin da daya da ke cikin jihar , kakakin majalisar dokoki na jihar mamba Sama’ila Abdulmuminu Kamba tare da sauran mambobbin majalisar dokokin, sakataren gwamnatin jihar ta Kebbi Alhaji Babale Umar Yauri da mambobin majalisar zartarwa na jihar da kuma dattijan jam’iyya da kuma sauran su dukkan su sun samu halartar taron tattaunawa da aka gudanar a fadar gidan gwamnatin jihar na Kebbi a jiya a Birnin-kebbi. Inda dukkan su sun amince da shirya gudanar da zaben fid da gwani na jam’iyyar ta APC a jihar ta hanyar yin sulhu. Haka kuma uwar jam’iyya ta jihar ta tabbatar da cewa “duk wanda ya halarci taron na tattaunawa da a gudanar a jiya yasan ya hannu a takardar domin nuna amincewar sa kan matayar da aka cim ma yayin tattaunawa
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: