APC Ta Yi Tir Da Sakamakon Zaben Kananan Hukumomi Da A Bauchi

kananan hukumomi

Daga Khalid Idris Doya

 

Jam’iyyar APC a jihar Bauchi ta kalubalanci sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar Asabar da ta gabata, da cewar, wata babbar yaudara ce ta siyasa da tsabagen shegan-taka na son zuciya da gwamnatin PDP ta shirya.

A wani taron manema labarai da jam’iyyar ta gudanar a jiya, ta ce duk wani mutum da ya yarda aka rantsar da shi da nufin wai ya ci zabe bisa ga tsarin jam’iyyar PDP da hukumar zaben gwamnatin wannan jam’iyya, ya san yana yaudarar kansa ne kawai, kuma zai zanna ne bisa haramtacciyar kujerar mulki wacce ba ta da amincewar jama’an jihar.

Idan za a iya tunawa dai, hukumar shirya zabe ta jihar Bauchi mai lakabin ‘BASIEC’ ta gudanar da zaben a kananan hukumomi guda ashirin na jihar, inda ba tare da fayyace wadanda suka yi nasara a hukumance ba, kawai aka rantsar da wasu ‘yan takara da zummar cewar, sune suka lashe zabe.

Shugaban jam’iyyar a jihar Uba Ahmed Nana shine ya jagoranci taron ‘yan jaridan, ya ce ba za su shiga sharo ba shanu ba na zuwa koton jin kararrakin zabe wanda aka kaddamar ranar 13 ga watan Oktoba, 2020 ba domin sun san ba za yi masu adalci ba.

Alhaji Uba Nana don haka ya yi kira wa hukumomin tsaro da su mutunta ayyukan da tsarin mulkin kasar nan ya ba su na tsare rayuka da dukiyoyin jama’a, ba tare da son zuciya ko shiga sharo ba shanu ba domin gudun wulakancin gwamnati ko zama karnukan farautar ta ba.

Jam’iyyar APC ta ce “A bisa wannan mummunan sakamako na zaBe da jam’iyyar PDP ta shirya, muna kira ga dukkanin ‘ya’yan APC da masu ruwa da tsaki masoya jam’iyyar da kada su dauki doka a tafukan hannayen su, domin ita jam’iyya tana kokarin dukkanin iyawa na ganin cewar, ba’ayi maka fashi da rana ba.”

Nana ya bayyana zaben da aka gudanar na kananan hukumomi da cewar, zane ne da gwamnati PDP ta zayyana na son zuciya da kin gaskiya domin ta tauye wa masu jefa kuri’a hakkokin su na ‘yanchin ‘yan kasa na zaben shugabanni da zuciyoyin su suka aiyana masu.

Ya kare da cewar, “A matsayin ta na jamiyya, APC ta yi tir da sakamakon wannan zabe wanda ya kasance tamkar yin fashi ne da rana tsaka wa masu jefa kuri’a, kuma za ta yi kokarin ganin cewar, ta kwaci hakkokin ta”.

Uba Nana ya kuma ce an tafka magudi a dukkanin rumfunan zabe tare da zargin cewa ko kai kayan gudanar da zaben wasu rumfuna ma ba a yi ba amma an shelenta wanda ya ci, sannan ya nuna bacin ransu da yadda PDP ta shiga ta fita wajen ganin ta tafka magudi ta halin ko kaka.

Ya ce, suna nan suna shirin daukan matakan da suka dace domin kwato wa ‘yan takaransu da magoya bayansu hakkinsu, inda ya kuma jinjina wa ‘yan takaransu da suka shiga zaben tare da nemansu da su cigaba da biyayya wa uwar jam’iyyar domin ta ci gaba da kare musu kimarsu a kowani lokaci.

Ya kuma ce PDP za ta riski magudin da ta tafka nan gaba, “Jama’a sun fusata sosai da yadda suka ga magudi a rana tsaka.”

Exit mobile version