Bello Hamza" />

APC Ta Yi Watsi Da Zaben Da Za A Sake A Adamawa

Jam’iyyar APC ta yi watsi da zaben da INEC ta shirya gabatarwa gobe Alhamis 28 ga watan Maris a jihar Adamawa, an dai shirya gudanar da zaben da ba a kammala na gwamna bane a wasu sassan jihar.
Sakataren tsare tsaren jam’iyyar na jihar, Alhaji Ahmed Lawal, ya sanar da wannan shawarar tasu a tattaunawarsa da ‘yan jarida jiya Talata a garin Yola.
Lawal ya bayyana cewa, INEC bata tuntubi jam’iyyar ba kafin ta fitar da sabon ranar gudanar da zaben.
Ya yi zargin cewa, sun samu labarin sake zaben ne a kafafen watsa labarai na cewa, za a gudanar da zaben a ramar Alhamis 28 ga watan Maris.
“INEC ta kasa tuntubar jam’iyyun siyasar dake da ruwa da tsaki kafin ta sanya sabon ranar da za a gudanar da zaben.
“A saboda haka muna dari dari a kan rade radin da ake yawo da shin a cewa, za a gudanar da zaben da aka kasa kammalawa a ranar Alhamis, kuma daga dukkan alamu lamarin ya zama gaskiya.
“Bama tsoron zaben da za a gudanar amma ya kamata INEC ta yi abin da ya kamata.
“Ta yaya za a sanya gudanar da zabe a ranar aiki, ko ba a son ma’aikata su shiga harkar zaben bane.
“Zamu mika kokenmu ga babban ofishin INEC ta kasa a kan lamarin,’’ inji shi.
An ruwaito cewa, babbar kotun Adamawa ta bayar da hukuncin janye hana INEC gudanar da zaben da ta yi tun da farko, a halin yanzu INEC ta sanya gobe Alhamis 28 ga watan Maris don gudanar da zaben.

Exit mobile version