Abdulazeez Kabir Muhammad" />

APC Zata Nakasa Kafin 2023 Muddin Ba A  Takawa Oshiomole Birki Ba –Rochas

A jiya Litinin gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya gargadi Jam’iyyar APC cewar za su iya rasa tudun dafawa a shekarar 2023, idan har ba’a yi gyara ba akan yadda shugaban jam’iyyar na kasa, kwamred Adams Oshiomole ya ke tafiyar da al’amuran jam’iyyar.
Gwamna Rochas, ya kausasa harshe akan shugaban jam’iyyar su da cewar mummunar rawar da ya ke ci gaba da takawa, a bisa kujerar jagoranci ita ce ummul aba isin da ta sanya jam’iyyar APC ta sha kaye a wasu jihohin inda ta gaza rike kujerun ta yayin zaben da aka gudanar, Okoracha wanda a halin yanzu ya ke ci gaba da fafutikar samun takardar shaidar cin zaben Sanatan shiyyar Imo ta Tsakiya a hannun hukumar zabe INEC, ya yi wannan furucin ne a wata ganawa da yayi da manema labarai bayan ganawar sirrin da suka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Ya yi tsokaci dangane da yadda jam’iyyar APC ke gudanar da al’amurranta na samar da shugabanni a sabuwar Majalisar tarayya, inda ya yi ikirarin cewa jam’iyyar ta mai she da yankin Kudu maso Gabashin kasar nan tamkar saniyar ware, Okoracha ya ce nuna wariya ga yankin Kudu maso Gabas na daya daga cikin dalilai da za su jefa rudani a jam’iyyar APC da hakan zai yi tasirin gaske wajen kifewar ta yayin babban zaben kasa na 2023.
‘Wannan kasar bazata samu daidaito ba in har ba’a tafi a ‘yan Kudu maso gabas ba a cikin gudanar da al’amuran majalisar tarayya ba’. inji shi.
Exit mobile version