APGA Ba Ta Goyon Bayan ‘Yar Tinke – Shugaban Jam’iiyar Ta Jihar Neja

APGA

Daga Muhammad Awwal Umar,

Jam’iyyar APGA a Jihar Neja ta bayyana cewar ba ta goyon bayan zaben ‘yar tinke da majalisar tarayya ke yunkurin ya zama doka a babban zaben 2023 mai zuwa. Shugaban jam’iyyar a Jihar Neja, Alhaji Musa Liman ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wani zaman majalisar zartarwar jam’iyyar ta jihar da ya gudana a karshen makon a sakatariyar jam’iyyar da ke Kpakungu, Minna.

Musa Liman ya ce har yanzu siyasar kasar nan ba ta da karfin da za a ce zaben ‘yar tinke zai zama doka, domin yunkuri ne na rushe kananan jam’iyyu masu tasowa.

Ya kara da cewa wasu zababbun ‘yan majalisa ne da suka samu damar zuwa majalisa suka tara kudi suke kokarin ganin sun danne ‘yan siyasa masu tasowa.

“Idan an ce zaben ‘yar tinke ya zama doka, ‘yan takarkaru na wa ne ke da kudaden da za su iya tara magoya bayansu dan samun tikitin takarar zabe, saboda haka ba mu amince da wannan kudurin na ‘yan majalisun tarayya ba.

“APGA ba ta fargaba, domin kowa jam’iyyar ta taka rawar gani a zaben gwamna a Jihar Anambara, kuma kowani dan jihar nan ya ga rawar da dan majalisar tarayya mai wakiltar Rijau/Magama ya taka dan kankanin lokaci na zuwansa majalisar wakilai.

Da take karin haske, shugabar mata ta jam’iyyar ta jiha, Zuwaira Isah Ajiyah ta ce jam’iyyar APGA a shirye take domin fitar da kitse daga rogo wajen bai wa mata damar samun tikitin takara, domin kashi 80 na kuri’un da ake jefawa a jihar, mata ne ke ba da su, amma da zaran an ci nasara sai a mayar da su baya.

Exit mobile version