Zubairu T M Lawal" />

APGA Za Ta Lashe Zaben 2019 A Nasarawa, Inji Maku

Sakataren Jam’iyyar APGA na Kasa kuma dan takarar Gwamnan Jihar Nasarawa Hon. Labaran Maku ya bayyana a lokacin da ya ziyarci kauyen garin Mai akuya inda dubban jama’a suka tarbe shi a lokacin da yaje taron bude alunan hotan takararshi .

Labaran Maku ya ce ; Gwamnan Jihar maici yanzu baiyiwa al’umman Jihar komai ba .duk alkawarin da ya dauka na cewa ;zaiyi masu idan ya zaman Gwamna baiyi ko daya ba.

Maku ya ce ; al’umman Jihar Nasarawa suna cikin matsala ga rigingimu da ya jefa al’umman Jihar suna fama da yake yake .anata kashe jama’a Gwamnati ta gagara daukar matakin da zai kare rayuwansu.

Maku ya ce ; al’umman Nasarawa suna bukatar canjin gwamnati saboda suna bukatar kayayakin mure rayuwa amma wannan Gwamnatin ta jefa jama’a cikin wahala.

Ya ce ; yanzu al’umma suna tururuwa zuwa Jam’iyyar APGA saboda itace kadai zatakai ga tudun mun tsira.

Labaran Maku yayi kira ga Jarman Jihar Nasarawa da kada su kuskure su shige rigan yan siyasa masu amfani da addini. Ya ce ;wadanana YAN siyasa ba mutanin kirki bane basu da bukatar cigaban al’umma kansu kadai suka sani . idan ku ka zabe su babu aikin da za su yi iyaka su gina kansu.

Maku ya ce;rashin adalci irin ta APC harda wadanda suke cikinta takeyi masu .ya ce;a zaben Kananan hukumomi da Jam’iyyar APC ta shirya kuma a zaben fitar da gwani da Jam’iyyar tayi an samu rigingimu mai yawa cikin Jam’iyyar. Ya’yanta dayawa sun koka saboda cutar dasu da aka yi.

Haye;idan APGA ce take gudanar da Muliki a Jihar nan idan zaben Kananan hukumomi yazo za a bar kowa ya gudanar da irin rawar da zai iya takawa .

Amma dayake Jam’iyyar APC jam’iyya ce ta mayaudara suna yaudarar al’umma har ma da wadanda suke cikinta .yanzu ga shi Jam’iyyar APGA tana kara samun goyon baya ga dubban jama’a maza da mata sunata tururuwa zuwa cikinta .

Ya kara da cewa ; Jam’iyyar APGA ce zata kawo Zaman Lafiya a Jihar Nasarawa ta yadda kowa zai gudanar da harkokinsa ba tare da fargaban fadace-fadace ba.

Zaman Lafiya zai samu manoma da makiyaya za su yi hulda da kaywawan mu’amala da juna .

Labaran Maku ya ce ; yana godiya ga Allah yadda ya samu kyakkyawan yabo wajen al’umman Jihar Nasarawa sun shaideshi da cewa shi mutumin kirkine mai son Zaman Lafiya.

Labaran Maku ya fude sabin alluna mai hutonsa na takarar Gwamnan a shekarar 2019 wanda al’umman Lafia ta kudu suka Samar a gurare dabam dabam tundaga Akurba har zuwa Mai Akuya.

 

Exit mobile version