MUƘALAR YAU:
Aliyu Dahiru Aliyu +2349039128220 dahiraliyualiyu@gmail.com
Rubutun da na yi na makon da ya gabata shi ne wanda na fi kowanne rubutu da na yi a wannnan jaridar samun saƙonnin tambayoyi da kuma waɗanda suka nemi na kara sharhi ko fadada bayani akan muƙalar da na gabatar. Ummulkhairi Muhammad, wata ɗaliba a Jami’a, ta bayyana hakan da cewa yana da muhimmanci ganin cewa a yanzu duniya tana magana ne akan haƙƙoƙin ɗan Adam da kuma ‘yancin da yake da shi na aikata wasu abubuwan a rayuwarsa. Na samu saƙonni dayawa ta hanyar imel ɗina da kuma ta hanyar kira ko kuma saƙon tes. Wanda na ga yana da kyau na amsa a jarida shi ne wanda ya tambayeni alaƙar yancin ra’ayi da kuma iliman Falsafa. Tare da cewa bayani a ilimin Falsafa abu ne mai matuƙar faɗi, to amma zan ɗan kokarta ta yadda za’a fahimci saƙon cikin sauƙi. Don haka zan ƙara fadada bayanin maganar haƙƙoƙin ɗan Adam ta hanyar duba a iliman Falsafa, Kimiyya da kuma zamantakewa ganin dama kusan duka suna tattare wajen isar da saƙo daya ne. Daga ƙarshe sai na auna da yadda hakan zai taimakamana wajen fuskantar matsalolinmu a Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.
Zamantakewa ita take kawo banbancin ra’ayi da fahimta. Tun asali Plato ya gano cewa babu yadda za’a yi mutane su zamo masu ra’ayi iri ɗaya matuƙar suna da mabanbantan mafuskanta. Abin da kai kake gani dai-dai ne to waninka a kuskure yake ganinsa. Herodotus, babban masanin tarihin nan, ya bada labarin sarki Darius I (550-486 BCE) na kasar Greeks ya kirawo wasu mutanen kasar sa da suke da al’adar ƙona gawarwakinsu ya umarcesu da cewa nawa zai basu domin su cinye gawar! Duka gurin hankalinsu ya tashi. Daga baya ya kira wasu mutanen da suke cinye gawar mamatansu yace nawa zai basu don su ƙona gawar! Suma hankalinsu ya tashi. Daga nan sai ya tara mutanensa ya gayamusu cewa su dinga yiwa jama’a uzuri wajen bayyana ra’ayinsu. Abin da wasu suke ganinsa dai-dai to wasu suna ganinsa a kuskure. Daga nan bukatar barin kowa ya yi fahimtarsa ba tare da an tsangwame shi ba ta taso. Don haka bayan yakin duniya na biyu a shekarar 1948, majalisar dinkin duniya ta yi tunanin a fitar da wata hanya da za’a bawa kowanne ɗan adam haƙƙinsa ba tare da ya tsangwami wani ba.
Haka dai sashi na sha takwas na kundin shekara ta 1966 ya yi bayanin haƙƙoƙin da suka shafi zaman gari da kuma siyasa (The international coɓenant or ciɓil and political rights of 1966). Ya yi bayanin kamar haka :
- Kowane mutum yana da haƙƙi da ‘yancin tunani, ra’ayi da addini. Wannan haƙƙi ya tattare yancin mutum na ya yi addinin da yake so, da yancin ya yi imani da wani addinin da ya zabarwa kansa, da kuma yancin bayyana addinin ta hanyar ibada, taruka da munasabobi da kuma koyar da addini ko a cikin jama’a ko a daidaiku.
- Bai halatta a tilasawa wani akan lallai sai ya bi wani addini ba ko kuma a tilasta masa sai ya bar wani addini ba.
- Bai halatta a hana mutum yancin bayyana addininsa ba ko aƙidunsa sai da wasu dalilai na dokokin shari’a, waɗanda za su zamo bisa hujjar kare lafiyar jama’a, tsarin kasa, ladubban yan kasa da kuma haƙƙoƙin sauran jama’a.
Abin da yake a zahiri shi ne ‘yancin ra’ayi na kan gaba kafin a zo maganar yancin addini. Dole sai mutum ya zabi ra’ayinsa kafin ya zabu addininsa domin ra’ayi shi ne yake kaiwa ga bin wata hanya ta addini. Kuma shi ra’ayi yana canjawa ne daidai da karfi ko raunin mutum wajen wasu dalilai da suka shafe shi kamar ƙoƙarin bincike, yawan karatu, tattaunawa da muhawara, gwaje-gwaje da jarrabawa, wahalar rayuwa da dadinta da kuma sauran abubuwan da su ne suke sanya mutum canja ra’ayinsa. Don haka a koda yaushe ra’ayi yana canjawa to ya zama wajibi a bawa mutum damar canja ra’ayinsa kuma a bashi kariya daga hare-haren da zai fuskanta.
Abu ne da ya dace abar ra’ayoyi, tunani da fahimtocin addini domin mabiya su auna su maimakon a bar wata fahimta tana kokarin danne ra’ayin wata da makami ko ta tilas. Wannan kam shi ne hanya guda da ‘yan kallo daga waje zasu iya gane rarraunan ra’ayi da mai karfi. A “Areopagitica”, wani guri da aka tattauna batun ‘yancin watsa labarai da kuma aikin jarida, a shekara ta 1644 John Milton ya rubuta cewa : abar kowane ra’ayi da aƙida ta bayyana kanta akan ƙasa, a bari gaskiya tayi halinta a zahiri. Idan muka yi kokarin hana wata aƙidar to hakan ya shiga haƙƙinta wajen rage ƙarfinta. A bari kowace karya ta yaki gaskiya har sai an gano tabbas gaskiya gaskiya ce daga ƙarshe. Duka abin da na lissafa a sama na yi magana ne akan abin da ya danganci shari’a domin ya kasancemin wata shimfida wajen tattauna hakan a babin Falsafa.
Ta fuskar Falsafa, maganar yancin ra’ayi, na tunani ko na addini, yana duba ne bisa haƙiƙar yadda mutum zai zamo mai cikakken yanci ba tare da ya samu tilastuwa ta wata fuskar ko ta wata ba. Fuskokin kuwa sun haɗa da na zahiri da na baɗini. Hanyar Falsafa ta tattare wasu iliman da yawa kamar ilimin ƙwaƙwalwa da gabban jiki (Neuroscience and Physiology), ilimin zamantakewa da jama’a (Sociology and Anthropology), ilimin tattalin arziki musamman ɓangaren markisiyya (Marɗism) da ta tattare abubuwa da yawa akan iya ina mutum yake da yanci? Shin ɗan Adam yana da yanci ma kuwa? Idan da akwai ta yaya zai bayyana shi?
A ƙarni na 20 aka ƙara samun ci gaba ta ɓangaren bincike a ƙwaƙwalwar mutum don gano alaƙarsa da yancin tunaninsa ko bayyana ra’ayinsa. Aka fara bincike wajen daukar hoton ƙwaƙwalwa a lokacin da take tunani ta hanyar “PET- Positron-emission tomography” da kuma “FMRI- Functional Magnetic Resonance Imaging”. Ta haka malaman Kimiyya suka kara samun wasu abubuwa da basu yi tsammanin samu ba a ilimin ƙwaƙwalwa a lokacin da take tunani har aka samu wani sabon ilimin mai zaman kansa da aka kira da “cognitiɓe neuroscience” wanda zamu iya cewa ilimi ne da yake bincike akan tushen yadda ake tunani da ganewa (wajen bayyana ra’ayi) bisa tunzurin ƙwayoyin ƙwaƙwalwa.
Ina jin tsoron yin bayani mai faɗi akan wasu lamuran na Falsafa saboda faɗin iliminta da kuma zurfin da take dashi. Ina gudun kada bayani akan Falsafa ya janyo na fita daga gundarin abin da nake son isarwa. Ilimin Falsafa yana da faɗi sosai musamman saboda kasancewarsa uwa uba ga kowane ilimi na baya da na zamani. Don haka zan yi bayani ɗan kaɗan kamar yadda aka neme ni ba tare da na yi nutso sosai wajen kawo kowane ɓangare na Falsafa akan yancin ra’ayi ba, sai dai duba ga abin da ya shafemu a matsayin yan Arewa ko yan Nijeriya baki daya. Fata na dai Allah yasa jama’a su fahimta don su bawa kowa yancinsu kuma su ragewa kansu tsattsauran ra’ayi. Kafin mu kira gwamnati ta yi wani abu akwai buƙatar mu fahimce shi tukun akan kanmu domin canji da ni da kai ya fara kafin ga gwamnati.
Zamu ci gaba…