A cikin makon daya gabata ne dandamalin masu yada labarai da harshen Hausa su ka karrama mataimaki shugaban kungiyar Yan gwari ta kasa a garin Danja da ke jihar Katsina.
Wakilinmu na daya daga cikin wakilan kafafafen yada labarai da su ka halacci taron a wannan rana.
Ga rahoton da ya aiko Mana dashi kamar haka:
Taron an gudanar da shi ne a bubban dakin taro na cibiyar koyar da ilmin shugabanta da zamantakewa da ke garin Kudan wato citizens an Leadership hall.
Bayan da manyan baki sarakuna da Yan siyasa daga bangarori daban daban har da mawaka su halar ta ne sai wanda ya jagoranci dandamalin kwamret U.I Samaru ya gabatar da jawabin makasudin da yasa Arewa Hausa Reporters Forum zasu karrama shi mataimakin kungiyar Yan gwari ta kasa wato Alhajin Hamisu Malam Danja a wannan rana.
Daga cikin bayanan kwamret I.U Samaru yace, mataimaki shugaban kungiyar Yan gwari ta kasa zai Sami karamcine bisa yadda bicike ya tabbatar cewa Yana da kishin ci gaban kasa a bangaren taimakawa matasa ta bangarori da dama na rayuwa.
Ya kara da cewa, Alhaji Hamisu Malam na daya daga cikin wanda su ka taimaka wajan tabbatar da kasuwar tumatur ta garin Danja ya wanzu Wanda a halin yanzu ake alfahari da ita a fadin Arewa da Afrika Baki daya.
Kwamret I.U Samaru yace wannan dabi’a ta Alhajin Hamisu Malam itace ake bukatar shugabanni su rinkayi a cikin jama’ar su yace farfado da kaduwar tumatur ta Danja ya kawo cigaba Mai yawa a bangarori da dama ciki har da taimakawa Gwamnati wajan samawa matasa abin yi da ya rage matsalar kalubalen tsaro a yanki.
Ya ce, hakan ne yasa Arewa Hausa Reporters Forum zata karrama Alhaji Hamisu Malam, a matsayin (Garkuwan Matasan Danja) don bashi kwarin guiwa.
Hahaji Yazid Sadik shine sarkin Fulanin Danja kuma shine Uban Taro a lokacin da ya ke nasa jawabin sai ya fara da godiya ga Allah madaukakin sarki kuma yayi sallati ga Annabin rahama Muhammad tsira da aminci su tabbatar a gareshi.
Bayan haka yayi jinjina ga Arewa Hausa Reporters Forum bisa kara da su ka nunawa karamar hukumar Danja da Jihar Katsina baki daya bisa karrama Danmu Alhaji Hamisu Malam mataimakin Shugaban karamar Yan Gwari na kasa baki daya yace, hakan ya zama darasi ne ga Yan baya da cewa ashe duk abin da mutum ya ke yi Jama’a na kallonsa! yace sunji dadi sosai Allah ya bar zumunci ya kuma mayar da kowa gida lafta
Shi ma kwamishinan lafiya na jihar Katsina Injiniya Yakubu Nuhu a nasa jawabin ya nuna jinjina ne ga Arewa Hausa Reporters Forum bisa karamta abokinsu da sukayi, kuma yayi fatan alheri tare da yi masu addu’a ta musamman bisa kokari da girmamawa da su ka nunawa abokin su a karamar hukumar Danja da jihar Katsina Mai tarin albarka.
Bayan Shugaban kungiyar Yangwari ta kasa Alaramma ya mika kambin karamcin ga Alhaji Hamisu Malam ne gurin ya dauki Tafi da cewa da jinjina na nuna farin ciki da wannan karamcin da yazo was jama’ar Danja da kungiyar Yan gwari na kasa baki daya.
Karshe sai Alhaji Hamisu Malam yayi jawabin godiya tare da fatan alheri ga Arewa Hausa Reporters Forum kuma yayi fatan alheri ga dukkan jama’ar da su ka zo don tayashi murna.
Daga cikin Mayan Baki akwai Alhaji Rabi’u Kugiya O.6 da sakataren Kungiya yan gwari na Danja sai Alhaji Yahaya Shehu Bakori da Hajiya Fatima Malunfashi da dai sauransu
An yi taro Lafiya an tashi lafiya.