Connect with us

MAHANGA

Arewa Ina Muka Dosa? (II)

Published

on

A baya mun kalli Arewa da irin albarkatun kasa da Allah Ya albarkaci wannan yaki da su, kama ga Kuza da Dinare da Tama da karafa da kasar noma da yanayin da zai taimakawa noman. Sannan uwa Uba Allah Ya azurta yankin da zaman lafiya.

Dalilan da suka haifar rashin zaman lafiya sun hada da:

  1. Rashin jagorori nagari tsakanin shugabanin siyasa na wannan yankin.
  2. Zarmiya da rashin wadatar zuci na wasu daga cikin jagororrin addinai na wannan yankin
  3. Rashin kishin Arewar daga wasu daga cikin shugabannin kasa ‘yan Arewar.
  4. Fadace-fadacen addini tsakanin manyan addinai biyu da muke da su.
  5. Yawan fadace-fadacen kabilanci tsakanin manya da kananan kabilun Arewa.
  6. Fadace-fadacen makiyaya da manoma
  7. Rikice-rikice da ake kunno su don siyasa

Jagorori da suka jagoranci Arewa a baya, a kullum, tunaninsu shi ne Arewa kafin kansu, sannan a kodayaushe, tunaninsu mai za su yi wa Arewa da ‘yan Arewa, ba mai Arewa za ta yi musu ba, saɓanin shugabanin Arewa na yanzu, wanda kullum tunaninsu mai za su samu idan suka raɓu da Arewa da su da ‘ya’yansu.

Kowa ya kwana da sanin cewa, su Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato su Sir, Abubakar Tafawa Balewa su Gwamna Awong sarkin Kagoro, da su marigayi Sunday Awoniye, da su Isa Kaita Su Aliyu Makaman Bidda sun tafiyar da rayuwarsu a kan Arewa da ‘yan Arewa ba tare da nuna bambancin addini ko kabila ba, wadansunsu ma kashe su aka yi a kan suna kishin Arewar da ‘yan Arewar. Wannan ne ya sa Arewa ta samu aminci da daukaka da muhiba, sannan ta zauna lafiya ba tare da fadace-fadace na kabilanci ko addini ba. Amma a yau mafiya daga cikin masu ikirari da cewa su ne jagorori a Arewa suna yi ne don me za su samu ba mai za su samawar Arewa ba ta fuskar jagoranci, atakaice dai sun zama ‘yan gwagwar amiya ba ‘yan gwagwarmaya ba.

Sanin kowa ne a wannan yanki na Arewa, akwai Labi-labi da aka warewa Fulani don kiwo, amma wadannan da suke ikirarin su ne jagorori na mulki da siyasa sun yanyanka wadannan Labibbikan na kiwo sun mallakawa kansu a matsayin gidan gona da su da yaransu na siyasa, da wanda suke so. Wannan rashin Labikan yana daya daga abubuwan da suke haifar da fadan makiyaya da manoma, sannan yana daya daga abubuwan da suke sa makiyaya na wannan yankin zuwa wadansu yankunan na wannan kasa suna fuskantar gori da barazana ta rayukansu, kai hatta wadansu munanan dabi’u da ake zarginsu da aikatawa sun koyo su daga wasu yankunan kasar nan ne. Kuma kowa ya san cewa, idan ka cire noma sai kiwo.

A kwanaki baya shugaban kasa ya yi maganar ” riga settlement ” ko a ina aka kwana? Hakazalika, shugabanin addinai a mafiyawancin lokata, idan suka rabi shugabanni, amaimakon su dora a kan turba ta hanyar yi musu wa’azi sai su ɓuge da neman abin duniya saboda zarmiya da rashin wadatar zuci, wannan ne ya sa shugabannin ko jagororrin ba sa kwatanta adalci a jagorancinsu, wanda duk inda aka rasa adalci to ba zaman lafiya. Misali, su Sardauna sun ja malamai a jikinsu amma malaman ba a ga sun tara abin duniya ba a rana tsaka, sannan suma shugabannin ba su tara abin duniya ba yankin aka kalla da cigaban yankin da al’ummar yankin. Don haka, yankin ya zauna lafiya da al’umma dunkulliya.

Rashin kishin Arewar daga wasu daga cikin shugabanni kasa ‘yan asalin Arewar. Allah Ya azurta wannan yankin da shugabannin da suka mulki wannan kasar masu tarin yawa, sai ya zamana suka zama inuwar giginya ga ita kanta Arewar. Kamar yadda muka sani, baya ga wadancan ma’adanai noma da kiwo su ne jagoran tattalin arzikin Arewa kai da ma kasar baki daya kafin samun man fetur, amma da yawa daga cikinsu babu wanda ya fito da gaske don ya tallafi wannan noman domin ya zama kishiyar man fetur da samawa mutanen wannan yankin ayyukan yi domin kawar da talauci da zaman banza. Da haka noman ya wulakance aka rinka samun kwararowar mutane daga kauyuka zuwa burane, rashin aikin yi ya yawaita, laifuffuka da fadace-fadace suka yi yawa kai harma da rashin tsaro.
Advertisement

labarai