Connect with us

MAHANGA

Arewa Ina Muka Dosa?

Published

on

Arewa, yanki ne da ke Arewacin Nijeriya, wanda a yau ya kunshi jihohi goma sha tara. Wadannan jihohi haduwarsu ba ta yau ba ce, kusan shekaru dari biyu ko fiye suna tare a karkashin tuta daya ita ce tuta ta daular Usmaniyya bisa jagorancin Fulani masu jihadi. Jagoran wannan tafiya ta juyin juya hali, shi ne, Shehu Usman Dan fodiyo.
Bayan zuwan Turawa aka rarraba wannan yanki a matsayin Lardi-lardi bisa jagorancin Turawan mulkin mallaka, domin duk da cewa sarakuna ne ke mulki bisa tsarin da suka gada daga magabatansu, sai tsarin ya koma tsari ne da ake karbar ummarni daga Turawan mulkin mallaka. Yankin Arewa, yanki ne da Allah Ya azurta yankin da kasar noma, tare da filayen noma da dausayyiyika da koramu da tafkuna manya-manya. Ba ya ga haka, Allah Ya azurta yankin da yanayi da zai taimakawa kowanne irin nau’i na noman da ake bukata a yi a wannan yankin. Hakazalika, wannan yanki, Allah Ya azurta shi da ma’adanai, kama ga kuza a yankin Fulato Jos da dinare a yankin Zamfara, muna da kanwa a yankin kasar Borno da Yobe, haka idan ka dawo kasar Kano akwai ma’adanai a kasar Doguwa, sannan a Neja muna da kuza da dinare da sauransu.
Idan ka yi gaba, yankin yana da tama a kasar Lakwaja da ke jihar Kogi a yau. Haka idan muka dauki kowanne yanki na Arewa kusan babu wani yanki da Allah bai azurta shi da wani arziki na karkashin kasa ba.
Hakazalika, Allah Ya azurta wannan yanki arzikin bisashe wato shanu da akuyoyi da tumakai da raguna da sauran nau’ikan kwari da dabbobi kamar kaji da zabi da agwagi da talo-talo da dawisu sannan uwa uba ga filayen kiwon da yanayin da zai taimakawa kiwon.
Abin da duk ya fi wannan shi ne, wannan yankin, Allah Ya azurta shi da yawan jama’a ga al’ummu da kabilu daban-daban. Sannan a wanccan lokacin ga zaman lafiya a tsakanin kabilun.
Abin tambaya a nan shi ne,
Mene ne ya gadarwa Arewa tallaucin da ya addabi yankin?
Mene ne ya sa a yau ake samun yawan fadace-fadace tsakanin kabilun da suke zaune a baya cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali a baya?
Mene ne ya sa ake samun yawan fadace-fadace tsakanin manoma da makiyaya?
Mene ne ya sa ake samun yawan fadan addini a wannan yankin a yau?
Uwa uba mene ne ya sa a yau ake zaune ba tare da jagoranci a wannan yankin na Arewa?
Kafin mu shiga cikin amsa wadannan tambayoyi, za mu yi ratse da kawo wasu baitoci daga wakar “Arewa Jamhuriya, ko Mulukiya” ta marigayi Sa’adu Zungur da yake cewa,
” Sallama a gare ku sarakuna,
Mun yi niyyar bayyana gaskiya”
“Addu’armu ga Allah Rahimi,
Ya kiyaye Arewa gaba daya. ”
“Muminai da Masihai jumlatan
Kuma da arna dodannin giya”
“Totocin Shaihu Mujaddadi,
Goma sha biyu ne Najeriya. ”
“Sir Assidiku Abubakar,
Ga Arewa tana kan shan wuya”
“Hausawa su da Barebari,
Ai amana ce da kilefiya”
“Yalla za mu kiyaye har mu bar,
‘Ya’yanmu su gaji halaliya”
“Hakki na kabiloli duka,
Na wuyanku, ku sauke lafiya ”
“Daularku da kayin muminai
Da wasunsu, ta wanye lafiya ”
“Da aminci babu gwagwarmaya,
Babu zalunci da hatsaniya. ”
Wadannan baitoci shimfida ce, fashin bakin da amsa tambayoyin da suka gabata, sai a rubutu na gaba.

Advertisement

labarai