Asusun Kula da kananan yara ta Majalisar dinkin Duniya, (UNICEF) ya shaida cewar, akwai barazanar cewa, yara sama da 300,000 za su iya rasa rayukansu sakamakon cutar karancin abinci mai gina jiki, wato Tamowa, a shiyyar Arewa maso Gabas da ke Nijeriya a cikin wannan sabuwar shekarar, 2021.
UNICEF ta nuna fargabarta kan cewa kananan yara wadanda galibinsu ‘yan kasa da shekaru biyar ne, za su iya galabaita matuka a wannan shekarar sakamakon karancin abinci mai gina jiki a Nijeriya, lamarin da aka nuna da cewa zai fi tsamari a shiyyar arewa maso gabas.
A sanarwar da asusun kula da yara ta Majalisar dinkin Duniyar, UNICEF ya fitar, ya shaida cewar, ana harsashen sama da yara 800,000 ne za su yi fama da matsananciyar matsalar rashin abinci mai gina jiki a cikin wannan shekarar dukka a shiyyar arewa maso gabas.
Jihohin arewa maso gabas da wannan lamarin ya shafa sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Taraba, Gombe da jihar Bauchi wanda hare-haren ‘yan Boko Haram ya jigata shiyyar tun shekarun baya.
A cewar ofishin kula da hulda da kasashen waje, kungiyar ta’addan Boko Haram din ta kashe kusan mutum 70,000 tare da tilasta wa kusan mutum miliyan biyu da rabi 2.5m kaura da hijira daga muhallansu ciki har da yara kananan.
Suka ce, mutum kusan 250,000 ne aka bada rahoton sun yi gudun hijira daga Nijeriya zuwa kasashen Kamaru, Chadi da kuma Nijar domin tsira da rayukansu sakamakon hare-haren kungiyar ta’adda.
A sanarwar ta UNICEF na cewa, “A Arewa Maso Gabashin Nijeriya, sama da yara 800,000 ake tsammanin za su iya kamuwa da cutar Tamowa a wannan shekarar ta 2021, tare da kusan yara 300,000 da za su iya mutuwa sakamakon kamuwa da wannan cutar.”
UNICEF ya ce, bayan ma shiyyar arewa maso gabas, su ma jihohin da ke Arewa Maso Yamma da suka hada da irin jihar Kebbi yara kashi 66 cikin dari na fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.
“A jihar Sokoto, wanda ita ma ke arewa maso yamma, kashi 18 cikin 100 na fama da cutar Tamowa, yayin da kashi 6.5 na fuskantar matsananciyar karancin abinci mai gina jiki,” inji UNICEF.
UNICEF, ya bayyana matukar damuwa dangane da cewa yara kananan ‘yan kasa da shekara biyar fiye da miliyan 10.4 a wasu kasashen Afrika za su fuskanci tsananin matsalar karancin abinci mai gina jiki wato Tamowa a 2021.
kasashe da lamarin ya shafa sun hada da nan gida Nijeriya, Jamhuriyyar Nijar, Burkina Faso, Jamhuriyyar Dimokuradiyyar Congo (DRC), Sudan ta Kudu, da kuma Yemen.
“kasashen da ke fama da rikice-rikice, matsalar gurbacewar yanayi, tare da cutar Korona, yanzu kuma lamarin ya juya musu zuwa matsalar karancin abinci mai gina jiki wani karin bala’in da ke tafe,” Inji Babban Daraktan UNICEF, Henrietta Fore.
Wakazalika, UNICEF din ta yi hasashen cewa, za a iya haifar yara 21,439 a ranar 1 ga watan Janairu a Nijeriya, wanda hakan ya maida Nijeriya cikin kididdiga a matsayin kasa ta uku wadanda suka fi yawan haihuwa a sabuwar shekara.
A sanarwar da mai rikon mukamin wakilin UNICEF a Abuja, Renu Wadhwa ya fitar, ya yi kiyasin yara 371,504 ne aka haifa a ranar farko ta sabuwar shekara a duniya baki daya.
Sanarwar ta ce, kasar Indiya ce mai mafi yawan yaran da aka haifa a farkon sabuwar shekara wanda aka samu adadin sabbin yara 59,995, sai kuma China wanda aka haifi yara 35,615, tare da Nijeriya ta kasance kasa ta uku mai sabin yara 21,439 da aka haifa a ranar farko ta sabuwar shekara.
Hukumar ta kuma bada shawarar cewa akwai bukatar a himmatu wajen inganta rayuwar yara kanana a fadin Nijeriya lura da yadda rayuwarsu ke baya-baya ta fuskacin ingantuwa.
UNICEF ta ce, idan ba a tashi tsaye wajen inganta rayuwar yara kananan a Nijeriya ba, to lallai za su fada cikin mawuyancin rayuwa wanda hakan ke barazana ga lafiyarsu da rayukansu.
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya roki a samar da abinci wa ‘yan gudun hijira sama da 800,000 da suke cikin mawuyacin hali a sassa daban-daban 11 da ke jihar.
Gwamnan ya yi wannan rokon ne a shalkwatar hukumar samar da agajin gaggawa ta kasa NEMA da ke Abuja yayin ziyarar da ya kai a ranar Alhamis.
Zulum, wanda ya gabatar da wasika ga Darakta Janar na NEMA, Muhammadu Mohammed ya shaida cewa, ‘yan gudun hijira a Monguno, Bama, Damboa, Gwoza, Dikwa, Gamboru, Ngala, Damasak, Banki, Pulka da Gajiram su na tsananin bukatar tallafin abinci domin dafa wa kokarin gwamnatin jihar na cigaba da kula da rayuwarsu.
Gwamnan ya shaida cewar samar da tallafin abincin zai kai ga kyautata rayuwar ‘yan gudun hijiran wadanda mafi yawansu manoma ne da a halin yanzu sun rasa gonakansu sakamakon hare-haren ‘yan ta’adda.
Da ya ke maida jawabinsa, Darakta Janar na NEMA, Muhammad Mohammed, ya baiwa gwamna Zulum tabbacin hukumarsu na agaza wa ‘yan gudun hijiran.