Arewa Na Halaka Kanta Da Kanta – Sarki Sanusi II

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa, Arewacin Nijetiya za ta cigaba da tarwatsa kanta matukar ba ta sauya daga yadda ta ke a halin yanzu ba. Sarkin ya yi wannan furuci ne a ranar Litinin da ta gabata a Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna yayin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar Gwamnan Jihar Kaduna. Malam Nasir El-Rufai Shekaru 60.

Sarki Sanusi II ya ce, a matsayin shugaba, maimaita abinda ka tarar a na yi tare da tsammanin za ka bambanta da sauran, wannan ba daidai ba ne. Ya kara da cewa, canji kadai zai samu ne a Arewa, idan a ka fara yin abubuwa mabambanta.

Daga nan sai Sarkin ya jinjina wa salon gyaran bangaren ilimi na Gwamna El-Rufai tare da bayyana cewa, hakan ne kadai zai iya tseratar da Arewa daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta a ciki.

“Daidai ne idan gwamna ya bi salon da ya tarar na mulki a cewar mutanen Arewa, amma magana ta gaskiya ba daidai ba ne idan ya bi salon da ba zai kawo wani canji ga yankin ba.

Idan kuwa Shugaba ko mai mulki ya yi hakan, za mu iya cewa yana daga cikin matsalar wannan yanki.

“Babban canji a Arewa zai zo ne bayan mun gano cewa, sai mun banbanta da sauran. Sannan idan har Arewa ba ta canza ba, to kuwa ko shakka babu za ta afka cikin halaka. Idan har ba mu canza ba, akwai lokacin da mun sani dai sai ya zo” in ji shi.

Haka zalika, sauran yankuna a kasar nan na zuba makudan kudade domin ilimantar da yaransu tare da yaye dalibai daga manyan makarantu, amma mu ba mu damu da yin haka ba.

Sannan, wadannan yankunan ba za su zuba ido su kasa hayewa Shugabancinmu ba, saboda ba daga yankin da ya kamata suke ba, bayan mun gaza gina ‘ya’yanmu”, a cewar Basaraken.

Ya bayyana cewa, babu wani Shugaba a Arewa da zai samu farin ciki bayan yana zagaye da matsaloli a yankin. Arewa na halaka kanta da kanta ne. Babu wani Shugaba a Arewa da zai ce yau yana cikin farin ciki. “Ba za ka zama cikin farin ciki a Arewa ba bayan kashi 87 na talaucin Nijeriya na Arewa. Sannan babu yadda za a yi ka yi farin ciki bayan yara da yawa ba sa zuwa makaranta a dai wannan yanki. Kazalika, babu yadda za a yi ka yi farin ciki bayan akwai matsalar Boko Haram”, kamar yadda Jaridar the Cable ta ruwaito.

“Mu na taya Nasir murnar zagayowar ranar haihuwarsa kuma ba ma so ya yi farin ciki a matsayinsa na Shugaba. Saboda farin ciki na zuwa ne bayan da jiha ta kai wani mataki na daukaka tare da mutanenta.”

Har wa yau, ya ce ya kamata a taya El-rufai murna ne a matsayinsa na Jami’in gwamnati, wanda ke kokarin shawo kan manyan matsalolin yankinsa.”Idan aka duba yadda Gwamnan Jihar Kaduna ya yi da kasafin kudinsa, ta yadda kaso 40
ya tafi kai tsaye bangaren ilimi, za mu iya cewa wannan ce hanyar da za ta tseratar da Arewa,” in ji Sarkin Kano.

Exit mobile version