Abba Ibrahim Wada" />

Argentina Ta Sha Da Kyar A Gasar Copa America

Tawagar kwallon kafa ta Argentina ta kai karawar daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin kudancin Amurka ta Copa America wadda take gudana  a halin yanzu, bayan da ta doke kasar Katar da ci 2-0 ranar Lahadi.

Bayan da ta samu maki daya a cikin wasanni biyu a rukuni na biyu, tawagar Argentina na bukatar maki uku da zai ba ta damar kai wa zagayen gaba, hakan kuwa ta yi ta ci Katar 2-0 kuma Argentina de ta fara cin kwallo ta hannun Lautaro Martinez daga baya Sergio Aguero ya kara ta biyu.

Aguero ya samu damar kara kwallo a raga, amma ya kasa ci, shi kansa kyaftin Lionel Messi ya samu damar da zai zura kwallon a raga shi ma ta gagara kuma da wannan nasarar da Argentina ta samu za ta fafata da kasar Benezuela a wasan daf da na kusa da na karshe ranar Juma’a.

Dan wasan Argentina dai ta na shan suka daga bangarori da dama a duniya a gasar musamman dan wasa Leonel Messi wanda a ke yawan zargin cewa ba ya buga wasa da zuciya idan ya na bugawa kasar wasa.

Sai dai wasu kuma su na kare dan wasan wanda shi ne kyaftin din tawagar inda su ke ganin rashin ’yan wasan da za su taimaka ma sa ne ya sa ba ya kokari sai dai dan sai dai dan wasan da kansa ya bawa ‘yan kasar hakuri tun a wasan farko da sukayi rashin nasara a hannun kasar Colombia

Colombia ce ta ja ragamar rukunin farko, bayan da ta ci wasa uku a jere, inda a karawar karshe ta ci Paraguay 1-0 a Arena Fonte Noba, kuma Gustabo Cuellar ne ya ci kwallon yayinda itama Brazil ta samu damar fitowa zagaye na gaba a gasar ta bana.

Exit mobile version