Connect with us

WASANNI

Arsenal Da AC Milan Suna Fafatawa A Kan Luca Jovic

Published

on

kungiyoyin Arsenal da AC Milan sune akan gaba wajen ganin daya daga cikinsu ta samu nasarar daukar dan wasan gaba na kuniyar kwallon kafa ta Real Madrid, Luca Jovic, wanda yake fatan sake sabuwar kungiya a kakar wasa mai zuwa.
A kwanakin baya dan wasa Jovic, ya bayyana cewa baya son ci gaba da zaman kungiyar ta kasar Sipaniya kuma yana fatan tafiya kungiyar da zai dinga buga wasanni a duk sati hakan yasa ake ganin karshen zamansa yazo a kasar Spaniya.
Real Madrid dai ta samu nasarar sayan matashin dan wasan ne mai shekara 22 a duniya daga kungiyar kwallon kafa ta Eintracht Frankfurt ta kasar Jamus a watan Julin shekarar data gabata sai dai matashin dan wasan dan kasar Serbia kwallaye biyu kawai ya zura a raga cikin wasanni 24 daya bugawa kungiyar a wannan kakar.
kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ce ta fara nuna sha’awarta ga matashin dan wasan wanda  a yanzu haka yana jiyya sakamakon ciwon da yaji a kafarsa sai dai yafi son komawa kungiyar AC Milan ta kasar Italiya da buga wasa idan har zai bar Real Madrid sai dai Arsenal zata bashi albashin da yafi na AC Milan.
Shima dan wasan da kansa ya bayyana cewa baya son ganinsa a kungiyar ta Real Madrid a kakar wasa mai zuwa hakan yasa ya bawa wakilinsa umarnin cewa yana son ya samu kungiyar da zasu koma buga wasa a kakar wasa mai zuwa.
Da farko dai AC Milan tana fatan karbar aron dan wasan daga Real Mdarid na tsawon shekara biyu inda daga baya kuma sai ta biya kudinsa idan yayi abinda ake bukata inda zata biya fam miliyan 31.
Har ila yau, AC Milan ta amince zata bayar da kudi fam miliyan shida idan har za’a bata aron matashin dan wasan na tsawon shekara biyu kuma dan wasan da ita kanta Real Madrid suna fatan a cimma matsaya.
Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bayyana cewa idan har za’a sayar mata da dan wasan zata iya biyan kudinsa a lokaci daya hakan yasa ake ganin zata iya samun nasara saboda Real Madrid tana tsananin bukatar kudi sakamakon karayar tattalin arzikin da kungiyoyi suka samu saboda annobar cutar Korona.
Sakamakon rashin kudin da kungiyoyi suka shiga dalilin cutar Korona yasa ake ganin Real Madrid zata ci gaba da rike dan wasan nata idan har ba zata kashe kudaden da ake bukata ba wajen sayan babban dan wasan gaba sai dai idan za’a bata kudi a yanzu
Gaba daya kwallayen da Jovic ya zura a kungiyar a wasannin Laliga ya zura su, inda ya zura kwallo a ragar kungiyar Legannes a watan Oktoban shekarar data gabata sannan ya sake zura wata a ragar Osasuna a cikin watan Fabrairun daya gabata kafin a tafi hutun dole na Korona.
Advertisement

labarai