Connect with us

WASANNI

Arsenal Da Tottenham Suna Neman Eric Baily Na Manchester United

Published

on

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyoyin birnin Landan, Arsenal da abokiyar hamayyarta Tottenham suna zawarcin dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Eric Baily domin ya koma daya daga cikin kungiyoyin.

Baily dai rabonsa daya bugawa kungiyar wasa tun a wasanta na biyu na gasar firimiya datayi rashin nasara akan kungiyar Brighton Albion daci 3-2 wasan da ake ganin kamar yabada gudunmawa wajen rashin nasarar da kungiyar tayi.

Hakan yasa mai koyar da ‘yan wasan kungiyar Jose Mourinho bai sake saka dan wasan a wasannin kungiyar guda uku data buga ba da kungiyoyin Tottenham da Burnley da kuma wasan data buga a wannan makon da Watford.

An bayyana cewa Eric Baily, dan kasar Ibory Coast, zaiso barin kungiyar idan har yaga daya daga cikin kungiyoyin da suke kokari a gasar suna zawarcinsa idan har bai dawo cikin kungiyar ba ana amfani dashi a kowanne wasa.

Kungiyoyin Arsenal da Tottenham dai suna bibiyar dan wasan da halin dayake ciki kuma idan har abubuwa basu canja ba zasu nemi dan wasan a watan Janairun shekara mai kamawa idan aka bude kasuwar siyan ‘yan wasa.

Baily mai shekara 24 ya koma Manchester United ne daga kungiyar Billareal akan kudi fam miliyan 30 a shekara ta 2016 kuma tun bayan komawarsa kungiyar wasanni 37 kawai yabuga.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: