Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta, ya sake bayyana cewa akwai bukatar kungiyar ta sayo masa dan wasan gaba na Crystal Palace, Wilfred Zaha, dan kasar Ibory Coast, a watan Janairu mai kamawa.
Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace dai ta bayyana wa Arsenal cewa idan har tana son sayan dan wasanta na gaba sai ta biya fam miliyan 80 idan kuma ba haka ba sai dai ta bar mata dan wasanta.
A farkon wannan kakar wasan ne dai dan wasan ya bayyana cewa ya shirya barin kungiyar domin bugawa a babbar kungiya duk da cewa ya taba zaman kungiyar kwallon kafa ta Manchester United amma zaman bai yi masa dadi ba a lokacin tsohon kociyan kungiyar, Sir Aled Ferguson.
Kawo yanzu dai Arsenal ce kungiyar da ake ganin dan wasan mai shekara 26 a duniya zai koma kuma tuni ya roki shugabannin kungiyar dasu amince su fara Magana da Arsenal domin yasamu damar komawa babbar kungiya.
Sabon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dai yana ganin zasu iya sayan dan wasan akan fam miliyan 55 sai dai Crystal Palace ta bayyana cewa baza ta sayar da dan wasan ba kasa da Fam miliyan 80 farashin da zaiyi wuya Arsenal ta iya biya a halin yanzu musamman a watan Janairu da wasanni sukayi nisa.
Crystal Palace tana bukatar fam miliayn 80 akan dan wasan wanda ya zura kwallaye 10 cikin wasanni 35 din daya buga a kakar wasan data gabata hakan zaisa Arsenal bazata iya biyan kudin ba bayan da kungiyar ta sayi Nicholas Pepe fam miliyan 72 a farkon wannan kakar.
Sai dai Arsenal zata iya kara samun wasu kudaden ta hanyar sayar da wasu daga cikin manyan ‘yan wasanta kuma tuni aka fara rade radin cewa ta amince zata sallamar da wasu daga cikin ‘yan wasanta da suka hada da Ozil da Dhaka da kuma Lucas Toreira.