Connect with us

WASANNI

Arsenal Na Zawarcin Dabid Luiz Na Chelsea

Published

on

Rahotanni sun bayyana cewa sabon mai koyar da  kungiyar kwallon kafa ta Arsenal  ya fara zawarcin dan wasa Dabid Luiz na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea idan har bai samu damar daukar yan wasan da yake nema ba.

Dabid Luiz, mai shekaru 30 ya tsinci kansa acikin tsaka mai wuya  bayan wata matsala da suka samu da mai koyar da yan wasan kungiyar, Antomio Conte bayan kungiyar tasha kashi a wasan zakarun turai a hannun kungiyar kwallon kafa ta Roma daci 3-0 a kasar italiya a kakar data gabata.

Conte dai ya zargi Luiz da rashin dagewa a wasan wanda yasa kungiyar tasha kwallaye uku a raga inda hakan yasa mutanen biyu suka samu sabani da junansu.

Duk da haka dan wasan yana fama da rauni inda a yanzu kamar yadda Conte yafada dan wasan yana jinya kuma yana kan hanyar dawowa domin cigaba da buga wasanni a kungiyar.

Tun shekarar da Antonio Conte yakoma Chelsea ne dai ya siyo dan wasan daga kungiyar Paris Saint Geman bayan dan wasan yakoma kasar faransa da buga wasa daga kungiyar ta Chelsea lokacin Jose Mourinho.

Kungoyoyin Real Madrid da Barcelona ma suna zawarcin dan wasan dan asalin kasar Brazil wanda a yanzu haka yana murmurewa daga ciwon dayaji a kafarsa ta dama.

Tuni aka bayyana cewa kungiyar ta Chelsea ta shirya rabuwa da dan wasan a watan nan na janairu idan har ankaai tayin kudin da kungiyar take bukata.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta nuna sha’awarta ta neman dan wasan sakamakon itama kungiyar tana bukatar dan wasan baya a yanzu.

Tuni dai aka bayyana cewa mai koyar da kungiyar ta Arsenal, Unai Emery ya shirya tsaf domin taya dan wasan.

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: