Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Jose Mourinho, ya ce, tawagar ‘yan wasan Arsenal sun gasa wa ’yan wasansa aya a hannu, duk da cewa, su ne su ka yi nasara a wasan hamayya da a ka tashi Tottenham biyu Arsenal babu ko daya, inda ya jinjina wa takwaransa na Arsenal Mikel Arteta bayan wasan.
A minti na 13 da fara wasa Tottenham su ka saka wa Arsenal kwallon farko a raga, kwallon da dan wasa Son Heung-min ya narka a raga daga wajen da’ira ta 18 kuma kwallon da dan wasan baici irinta ba a wannan kakar.
Harry Kane ya mayar da wasa biyu babu ko daya, bayan da Son ya gara mai wata kwallo, shi ko ya shiga da gudu ya saka wa mai tsaron ragar Arsenal Bernd Leno, a daidai lokacin da ake daf da tafiya hutun rabin lokaci.
Wannan nasarar ta kai Tottenham saman teburin gasar firmiyar Ingila, kuma Mourinho na cewa ‘yan wasansa sun ji jiki a karawar sannan ya ce lallai babban wasa ne suka buga, kuma ba wai don da Arsenal a ka yi gumurzun ba.
Ya kara da cewa “Mikel Arteta babban mai koyarwa ne kuma matashi wanda nan gaba kadan zai zama babban mai koyarwa kuma ya burgeni saboda salon yadda yake buga wasa yana da kayatarwa sosai”
Wannan ne wasa na 11 da Arsenal ta fafata a gasar firimiyar Ingila inda ta samu nasara a wasanni hudu da canjaras guda daya sannan tayi rashin nasara a wasanni shida hakan yasa yanzu kngiyar take mataki na 15 akan teburin gasar firimiyar Ingila.