Arsenal Ta Fara Zawarcin Dembele Daga Barcelona

Daga Abba Ibrahim Wada

Rahotanni daga kasar sipaniya sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tafara zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ouseman Dembele domin yakoma kungiyar a kakar wasa mai zuwa.

Dembele, mai shekara 20 yakoma Barcelona ne daga kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund a farkon kakar da ake bugawa bayan da kungiyar ta biya fam miliyan 97 domin siyan dan wasan bayan sun siyar da Neymar zuwa kungiyar PSG dake kasar faransa.

Sai dai tun bayan komawar dan wasan Barcelona yake fama da rauni a kafarsa inda kawo yanzu wasanni uku kawai aka fara dashi acikin yan wasa na sha dayan farko sannan yabuga wasanni 6 wadanda yashigo bayan hutun rabin lokaci.

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mista Arsene Wenger, ya bayyana aniyarsa ta daukar dan wasan domin cigaba da gina kungiyar da sababbin yan wasa inda a watan Janairu ya dauki Aubameyang daga Dortmund din da kuma Mkhitaryan wanda shima yataba bugawa kungiyar Dortmund wasa a baya.

An bayyana cewa zuwan Coutinho Barcelona zai sa dan wasan bazai dinga buga wasanni akai-akai ba wanda ake ganin wannan dalilin zai saka dan wasan yafara tunanin komawa wata.

Exit mobile version