Arsenal Ta Kammala Daukar Timber
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Arsenal Ta Kammala Daukar Timber

bySadiq
2 years ago
Arsenal

Arsenal ta kammala daukar dan wasan baya na kasar Netherlands, Jurrien Timber daga Ajax kan kudi fam miliyan 34.

Farashin Timber zai iya tashi zuwa £38.5m idan aka hada da ‘yan tsarabe-tsarabe kuma dan wasan mai shekaru 22 ya koma Arsenal kan yarjejeniya mai tsawo.

  • Kiwon Lafiya: Yadda Dabi’un Ko-in-kula Ke Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuke
  • Gwamnan Sakkwato Ya Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Tambuwal

Zai kara karfafa tsaron Arsenal bayan dan wasan baya William Saliba ya amince da sabon kwantiragin shekaru hudu.

Kocin Arsenal Mikel Arteta, ya ce “Muna matukar farin ciki da Jurrien ya iske mu, shi din hazikin matashin mai tsaron baya ne.”

Jurrien matashin dan wasa ne, amma ya riga ya samu nasarori masu yawa,ya buga babbar gasa ta kasa da kasa fiye da sau daya.

Da kuma kofunan da ya lashe tare da Ajax. Muna fatan za a yi maraba da shigar da Jurrien cikin tawagarmu.

Ya buga wa Netherlands wasanni 15, ciki har da hudu a gasar cin kofin duniya da aka buga a Qatar, inda ya taimakawa tawagar Louis van Gaal ta kai wasan daf da na kusa da karshe.

Timber ya ce ya kasance mai sha’awar Arsenal a koyaushe wanda ya samo asali ne daga kaunar da yan uwansa ke nuna wa kulob din.

Timber ya ce ya kasance magoyin bayan Arsenal kullum, kuma ina son ganin Arsenal tana taka leda, suna da manyan yan wasa, yadda suke taka leda abin na burgeni.

Ina son kallon tsoffin yan wasan kungiyar Robin van Persie, da Thierry Henry Su ne yan wasan da na fi so inji shi.

Timber zai kara karfi ga bayan kungiyar Arsenal wadda ta zo ta biyu ga Manchester City a gasar cin kofin Premier da suka fafata a kakar da ta wuce.

Kuma ta samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai bayan shafe shekaru shida ba tare da sun shiga ba.

Timber ya buga wasanni 47 a dukkan gasannin da ya bugawa Ajax a kakar wasan da ta wuce,kuma ya taimakawa kungiyar Amsterdam ta lashe kofin Eredivisie a 2021 da 2022.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane
Wasanni

Ba Yanzu Zan Koma Gasar Firimiyar Ingila Ba – Harry Kane

October 7, 2025
Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni
Wasanni

Yanzu-Yanzu: Kwara United Ta Sallami Kocinta, Tunde Sanni

October 6, 2025
Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar
Wasanni

Kwallon Hockey: Nijeriya Na Fatan Samun Nasara A Masar

October 6, 2025
Next Post
Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?

Wane Ne Arda Guler Mai Lakabin ‘Sabon Messi A Real Madrid’?

LABARAI MASU NASABA

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version