Arsenal Ta Koma Zawarcin Chris Smalling

Daga Abba Ibrahim Wada Gwale

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tafara zawarcin dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Chris Smalling, dan kasar ingila domin ya maye mata gurbin Per Matersacker, wanda zaiyi ritaya a kungiyar a karshen kakar.

A kasuwar siye da siyar da yan wasan data gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta nemi dan wasan sai dai United din ta gayamata cewa dan wasan bayan nata bana siyarwa bane wanda hakan yasa kungiyar takoma zawarcin dan wasan baya na Westbrom, Jonny Ebans.

Manchester United dai ta bayyana cewa idan har Arsenal tana bukatar dan wasan sai ta biya fam miliyan 25 inda kuma Arsenal ta bayyana cewa bazata iya biyan abinda United din take bukata ba.

Sai dai watakila kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata iya siyar da dan wasan nata a karshen kakar nan sakamakon kungiyar tana son siyan sabon dan baya wanda bai kaishi shekaru ba.

Smalling yakoma kungiyar Manchester United ne a shekara ta 2010 daga kungiyar kwallon kafa ta Fulham dake kasar ingila inda kuma a wannan kakar yabuga wasanni 30 a kungiyar Manchester United.

Manchester United dai zata kara da kungiyar kwallon kafa ta Sebilla a gasar zakarun turai kuma watakila dan wasa Smalling yana daya daga cikin yan wasan da za su bugawa kungiyar wasa.

 

Exit mobile version