Arsenal Ta Na Fatan Cimma Yarjejeniya Da Celtic Kan Tierney

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tana fatan zata cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Celtic dake kasar Scotland akan dan wasan kungiyar, Kieran Tierney, wanda Arsenal din ta taya har sau biyu Celtic tana yin fatali da tayin.

Acikin satin daya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta taya dan wasan fam miliyan 13 Celtic tayi fatali da tayin sannan kuma ta sake tayawa 15 nanma Celtic din ta bayyana cewa dan wasanta yafi haka.

Tuni Celtic ta bayyanawa Arsenal cewa idan har tanason daukar dan wasan bayan nata sai ta biya fam miliyan 25 farashin da Arsenal take ganin yayi mata tsada sai dai an bayyana cewa Arsenal din zata sake komawa da sabon tayi na fam miliyan 18.

Kociyan kungiyar dai, Unai Emery bashi da kudaden da zai kashe domin sayan sababbin ‘yan wasa da yawa kuma masu tsada bayan da wasu rahotanni suka bayyana cewa shugabannin kungiyar sun ware fam miliyan 40 ga kociyan a wannan kakar.

Tierney dai zai dinga daukar albashin fan dubu 70 idan har ya amince ya koma Arsenal kuma zai fara bugawa kungiyar wasannin gasar firimiya kai tsaye sai dai wasu suna shakku kan kwarewar dan wasan wajen buga gasar firimiya.

Mai koyar da ‘yan wasan na Arsenal dai bai boye bay a bayyana cewa kungiyar tana bukatar sayan ‘yan wasa musamman a bay admin rage yawan kwallayen da ake saka musu a raga bayan da aka zura musu kwallaye 51 a kakar wasan data gabata.

Exit mobile version