Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Ta Shiga Zawarcin Luca Jovic Na Benfica

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta shiga zawarcin dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Benfica, Luca Jovic, wanda a yanzu yake zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Eintrach Frankfurt ta kasar Jamus.
Duk da cewa kungiyar ta Arsenal bata bukatar dan wasan gaba sakamakon ‘yan wasan gaba da kungiyar take dasu a yanzu irinsu Aledandre LacAzatte da kuma dan wasa Aubameyang Dan kasar Gabon amma kociyan kungiyar yana fatan samun dan wasan gaba matashi wanda zai dinga taimaka musu.
Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ce dai aka bayyana cewa a kwanakin baya ta shiga zawarcin dan wasan wanda dan asalin kasar Serbia ne yayinda itama kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara kallon dan wasan.
Kungiyoyin Chelsea da Real Madrid ma dai sun shiga neman dan wasan wanda ya shafe shekaru biyu yana zaman aro a kungiyar ta Frankfurt sai dai kungiyarsa ta Benfica tayi gargadin cewa dan wasan nata zaiyi tsada.
Jovic, wanda yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka wakilci kasar Serbia a gasar cin kofin duniyar da aka kammala a kasar Rasha ya zura kwallaye 21 cikin wasanni 32 daya bugawa kungiyar tasa a wannan kakar.
A watan daya gabata ne aka bayyana cewa dan wasan ya gama kulla yarjejeniya da Barcelona domin ya maye mata gurbin Luis Suares wanda shima yake shirin barin kungiyar a wannan karshen kakar sai dai bisa dukkan alamu har yanzu Barcelona bata cimma matsaya da dan wasan ba da kuma kungiyar sa.

Exit mobile version