Arsenal Ta Shiga Zawarcin Luiz Daga Chelsea

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake birnin Landan tashiga sahun manyan kungiyoyin da suke zawarcin dan wasa Dabid Luiz na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a watan Janairu.

Luiz, mai shekaru 30 ya tsinci kansa acikin tsaka mai wuya  bayan wata matsala da suka samu da mai koyar da ’yan wasan kungiyar, Antomio Conte bayan kungiyar tasha kasha a wasan zakarun turai a hannun kungiyar kwallon kafa ta Roma daci 3-0 a kasar italiya.

Conte dai ya zargi Luiz da rashin dagewa a wasan wanda yasa kungiyar tasha kwallaye uku a raga inda hakan yasa mutanen biyu suka samu sabani a  junansu.

Duk da haka dan wasan yana fama da rauni inda a yanzu kamar yadda Conte yafada dan wasan yana jinya kuma yana kan hanyar dawowa domin cigaba da buga wasanni a kungiyar.

Tun shekarar da Antonio Conte yakoma Chelsea ne dai ya siyo dan wasan daga kungiyar Paris Saint Geman bayan dan wasan yakoma kasar faransa da buga wasa daga kungiyar ta Chelsea lokacin Jose Mourinho.

Kungoyoyin Real Madrid da Barcelona ma suna zawarcin dan wasan dan asalin kasar Brazil wanda a yanzu haka yana murmurewa daga ciwon dayaji a kafarsa ta dama.

Tuni aka bayyana cewa kungiyar ta Chelsea ta shirya rabuwa da dan wasan a watan nan na janairu idan har ankai tayin kudin da kungiyar take bukata.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta nuna sha’awarta ta neman dan wasan sakamakon itama kungiyar tana bukatar dan wasan baya a yanzu.

Tuni dai aka bayyana cewa mai koyar da kungiyar ta Arsenal, Mista Arsene Wenger ya shirya tsaf domin taya dan wasan.

 

Exit mobile version