Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta kafa tarihin zama kungiya ta farko da ta fitar da Real Madrid daga gasar Zakarun Turai har sau biyu ba tare da Real din ta samu nasara akanta ba.
Manyan kungiyoyin biyu sun hadu sau 4 a tarihin gasar Zakarun Turai, inda Arsenal ta doke Real Madrid sau uku akayi canjaras1, Real Madrid ta kasa kai wa matakin na kusa da na karshe bayan ta yi rashin nasara da ci 5-1 a duka wasanni biyu.
Bukayo Saka ne ya jefa kwallo a ragar Madrid a minti na 65 na wasan bayan ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti 13 da fara wasa, Vinicius Jr. ne ya farkewa Madrid kwallonta mintuna kadan da cin da Saka ya yi, a mintunan karshe na wasan ne Martinelli ya jefawa Arsenal kwallonta ta biyu kuma ta karshe a wasan, inda aka tashe 1:2.