Arsenal za ta karbi bakuncin Cologne a wasan cikin rukuni a gasar Europa League a yau Alhamis.
Tuni kocin Arsenal, Arsene Wenger ya ce zai hutar da manyan ‘yan wasansa bakwai da suka hada da Peter Cech da Laurent Koscielny da Alexandre Lacazette da Granit Xhaka da Aaron Ramsey da Danny Welbeck da kuma Mesut Ozil.
A karon farko Jack Wilshere zai buga wa Arsenal wasa, bayan shekara daya, kuma Alexis Sanchez zai buga fafatawar domin ya dawo kan ganiyarsa a tamaula.