Mai koyar da yan wasan Arsenal, Arsene Wenger ya bayyana cewa har yanzu yana kan bakarsa na cigaba da canja yan wasa a kowanne wasa domin bawa wasu yan wasan damar buga wasanni sannan kuma wasu a basu damar buga wasa.
Mista Wenger ya bayyana hakane a jiya inda yace akwai yan wasan da yakamata ace sun buga wasa amma bazasu bug aba sannan akwai yan wasan da yakamata ace suna hutawa saboda hakan zaisa lafiyar yan wasan ta inganta.
A wannan shekarar dai mai koyarwar yana yawan canja yan wasa a kowanne wasa halin da wasu suke ganin kamar zaisa yan wasan su samu rashin tabbasa din buga wasa sannan kuma yan wasan bazasu gane kansu sosai ba,
Sai dai wenger yace wannan tsarin dayake a yanzu shine yadace da kungiyar a wannan lokaci kuma bazai canja ba domin yana ganin amfanin abin.
Arsenal dai zata fafata wasa da Brighton Albion a satin wasa na bakwai a inda ake tunanin yan wasa irinsu Lacazatte da Sanchez da Xhaka da ramsey duk zasu dawo cikin yan wasan farko a wasan wannan satin bayan daya ajiyesu a wasan cin kofin Europa da suka buga aranar alhamis din data gabata.