Abba Ibrahim Wada" />

Arsenal Za Ta Siyar Da Manyan ‘Yan Wasa Bakwai

Rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kociyan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Unai Emery, ya bayyana aniyarsa ta siyar da akalla ‘yan wasa bakwai daga cikin ‘yan wasan kungiyar domin samun kudin siyan ‘yan wasa biyu da yakeson karawa a tawagar sa.
Arsenal dai tuni da bazama a kasuwar siyan ‘yan wasa inda kawo yanzu tuni ta siyi ‘yan wasa da suka hada da Sokratis da Leno wanda mai tsaron raga ne sai kuma Stephan Leichesteiner daga Jubentus da kuma Lucas Torreira daga Sampadoria sai kuma Matteio Guendouzi daga kasar Faransa.
Rahotannin sun bayyana cewa sabon kociyan kungiyar yanason karin ‘yan wasa biyu da suka hada da dan wasan gaba na gefe da kuma dan wasan baya na gefen hannun hagu kuma yanason sai ya siyar da wasu ‘yan wasan domin samun kudin siya.
‘Yan wasanni uku da suka hada da Shkrodan Mustafi da Petr Cech da kuma Nacho Monreal du kana ganin zasu iya barin kungiyar duk da cewa a kakar wasan data gabata sun buga wasanni 110 a tsakaninsu
Ragowar ‘yan wasan da ake ganin kungiyar zata rabu dasu sun hadada Dannu Welbeck da Carl Jenkinson da Lucas Perez da kuma mai tsaron raga Dabis Ospina kuma ana saran Arsenal din za ta rage yawan ‘yan wasa bayan da a yanzu akwai ‘yan wasa 31 a kungiyar.
Arsenal dai zata fara buga wasanta na firimiya na farko da kungiyar Manchester City kafin kuma ta buga wasa na biyu da kungiyar Chelsea.

Exit mobile version