ASADUL MULUK

Muluuk

Da zance ya tabbata gaskiya, nan da nan sarki ya bayar da umarni akan jarumai su zauna cikin shiri, jama’a kuma su koma cikin gidajensu su kulle kofofi su ci gaba da addu’a, sannan ya ja kunnen duk mai dauke da makami ka da ya sake ya kai wa kowacce dabba hari in dai ba dabbobin ne aka ga za su fara barna ba. Dakaru suka fada cikin shiri kai ka ce za su fuskanci wata rundunar yaki ne, aka ware sahun gwanaye wajen iya harbi da kibau wadanda su ne aka bai wa dama da zarar sun ga zakuna sun fara barna to su fara harbi. Zakuna ba su shigo garin ba sai daf da lokacin Sallar walha, aka ga sun yo jerin gwano suna tafiya cikin nutsuwa, babbansu yana gaba da matarsa a gefensa ga ‘ya’yansu guda hudu suna dara, kai ka ce ba zakunan gaske bane.

Da suka zo dai-dai tsakiyar gari inda aka kafa tuta, sai babbansu ya daga kai ya yi nishi duk sai suka tsaya cak, daga baya suka yi wata da’ira suka sanya shi a tsakiya, suka zauna kamar tsawon rabin sa’a, ba tare da sun yi ko da wannan baban motsi ba, daga baya babbansu ya sake mikewa tsaye suka suka buda musu hanya shi da matarsa da ‘ya’yan suka wuce gaba aka ci gaba tafiya, yadda suka shigo lafiya, haka nan suka fita lafiya ba tare da sun taba kowa ba. Wani babban abin al’ajabi shi ne hatta dabbobi irinsu awaki da sauran irin su jakuna, da dawaki da sauransu, zakunan nan ba su kula su ba. Bayan sun wuce Sarki da sauran ‘yan majalisarsa suna biye da su a baya sannu-sannu aka raka su har can kan iyakar gari, jama’ar gari ma da suka samu labari ma su iya fita zuwa rakiya suka fito aka tafi tare da su, daga baya suka dawo gida.

An hakikance cewa wadannan zakuna sun kwararo ne daga Kudu maso Gabashin Kasar Huraasaana, daga cikin wata zazar wani babban dogarin Sarki Hasanul Basari, wanda ya ke mulkin kasar Huraasaana. Dama su kan yi irin wannan jerin gwano duk bayan shekara goma su fita shan iska, in ji masana tarihi, sai dai ba su taba ratsowa ta wannan kasa ba.

Exit mobile version