Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (32)

Shahid Ya Gana Da Shahida
Samirul’adlasi ya kwanta rashin lafiya mai tsanani har ta tsahon wata guda saboda juya masa baya da Hafida ta yi, tare da bakin cikin rashin tarayyarsa da Shahid, ga kuma uwa uba soyayya ta sarke tsakanin Shahid din da Shahida, yawaitar tunanin ne ya haifar masa da rashin lafiya.
To da yake an samu matsala tsakaninsa da Shahid, shi Shahid bai san halin da yake ciki ba, da fari da ya daina ganinsa ya yi tsammanin ko irin tafiyar nan ce sake yi wadda ya saba, irin wadda idan so ya motsa masa ya kan yi. Wani bawa daga cikin bayin sarki ne yake sanar da Shahid halin da Samir yake ci, don haka ya kudiri aniyar zuwa duba shi, ya shirya ya tafi gidan sarki.
Kafin ya kai ga zuwa inda Samir yake, ya wuce fada ya yi gaisuwa wurin sarki, sarki ya ce, me ya kawo shin gidan nan? Shahid ya kalli babansa waziri ya sunkuyar da kai. Waziri ya ce, kada ka dora min laifi, ka amsa wa mai martaba tambayar da ya yi maka. “ Na jima da gaya maka cewa komai ya wuce tsakanina da martaba, amma saboda zafin zuciyarka da ba ta manta abu sai yau ka zo”, sannan ya dubi sarki ya ce, Allah ya ba ka nasara, yau din ma fa abokinsa ya zo dubawa, don haka ka gan shi.
Sarki ya yi murmushi ya ce, na gode wa Allah tun da su ma a tsakaninsu yanzu babu wata gaba, dama ni su nake ji, “ Tashi ka je ka gaida abokinka na san idan ba kai ba babu wanda zai zo masa maganin cutarsa, Allah ya kara hada kanku.”
Ya tashi cikin kunya ya shiga cikin gida, a can ma ya wuce wurin matan sarki ya gaishe su, daga nan ya wuce zuwa dakin Samir, ya same shi kwance yana bacci, ya kalle shi ya ga duk ya rame kamanninsa duk sun sauya.
Ya zauna nan tsawon lokaci har sai da ya farka ya ganshi zaune bisa kujera, cikin mamki da kyar ya ce, kai ne a tafe yanzu? Shahid ya yi masa sallama ya ce, ni ne na zo duba ka, ban san b aka da lafiya ba, na yi tunanin ko ka yi tafiya ne da na ji shiru ba na ji motsinka. “ Samir haka duk ka lalace, saboda kaunar wadda ba ta sonka ba ta ko tunanin halin da kake ciki? Ya kamata mu sake tunani mu zauna mu yi shawara a tsakaninmu, idan da hali ka sauya wata budurwa a madadin Hafida.”
Samir ya ce, kana ganin haka za ta yiwu, kai fa wadda kake so a ranka za ka aura, ni kuma so kake na auri koma bayan haka? Shahid mu yi nazari kan haka mana, “ Na yi nazarin wannan soyayyar kuma na dawo daga rakiyarta, na yi alkawarin in har Allah ya tashi kafaduna daga wannan cuta da na dora wa kaina na son Hafida, to daga nan ba zan sake tunaninta a matsayin masoyiyata ba. kuma ina rokon ubangiji da ya musanya min ita da wadda ta fi ta alkhairi gare ni, yanzu a kan wannan kadamin nake.”
Shahid ya ce na yi farin cikin jin wannan kalami naka, ni kuma na yi maka wani alkawri, amma ba zan bayyana maka ba, sai na ga yadda tsayuwar kan wannan magana taka nan gaba.
“ Kai Shahid tun da na kwanta rashin lafiyar nan yau wata guda, ban taba samun sauki kamar yanzu ba, na samu karfi a jikina, ka ga babu abin da nake iya ci sai dai na yi ta shan ruwa da dabino, amma yanzu har na fara jin yinwa.” Shahid ya sa bayi suka kawo masa ruwan shayi da abinci, Shahid bai tafi gida ba sai da ya tabbatar da Samir ya ci abinci ya koshi, suka yi sallama ya koma gida.
Ishirin da biyu ga watan Safar ranar tarihi ce ga Shahida, domin ita ce rana ta farko da Shahida ya fara zuwa gidansu a matsayinsa na masoyinta. Yana isa kofar gidan sauka daga doki aka yi masa iso, aka shigar da shi cikin wata farfajiya da aka kawata ta farin labule ga tagogi nan iska na shigowa ko ta ina, ya zauna yana jiran zuwanta. Bayan wasu ‘yan dakikoki sai ya ji shigowar wani irin kamshin turare da ya shafe nasa a dadi, hakan ya alamta masa masoyiyarsa na kan hanya.
Abu na biyu da ya ji shi ne, sautin kayan karau, sarka, ‘yan kunnaye, da sauran kayan ado, sai ya gyara zama. Kujerar da za ta zauna tana fuskantar tasa, hadimai suka shigo da kayan ci da na sha irin gidan sarakai kamar yadda ta gani a gidansu sa’adda suka je duba shi. “ Ina marhaban da isowar wanda ruhina yake dauke da tunaninsa a ko da yaushe,” inji ta.
“Amincin Allah ya tabbata a gareki, na aminta da irin so da kaunar da kike yi min, ina alfahari da irin wannan mataki da na samu cikin ruhinki,” in ji Shahid. “ Kai yau sararin samaniya ya kara haske, ina ni’intuwa da kallon fuskar wanda zuciyata ke tsananin bege kafin saninsa da kaunar da nake yi masa, amma duk haka na san wata gimbiya ta rigaye ni samun muhalli cikin wannan zuciya.” Inji ta.
Ya ce, haka yake, kuma ba zan hana ki fadar abin da ke zuciyarki ba, saboda kwararowar kishi, amma ina son ki sani cewa, ita gimbiya zabin mahaifina ce, ke kuma zabi na ce da mahaifiyata da kannena, kazalika shi ma waziri ya yi na’am shigowarki cikin dangi, kin ga ashe ke zabin masarauta ce baki daya.”
“Aminiyata Hafida tana kwance rashin lafiyar sonka, wannan al’amari yana tsorata ni a duk sanda na je duba ta, yau kusan makonni biyu kenan, a mako na farko ma cikin kwanaki hudu na farko ba ta sanin wanda yake kanta. Amma dai yanzu tana samun sauki, ta haka ne ta ba ni sako a gareka cewa, idan har ka samu labarin kwanciyarta rashin lafiya, tana rokon ka da ka je ka duba ta don tana zaton cutar ba ta tashi ba ce.”
Sai ya ajiye abin da yake ci ya yi shiru zuwa wani lokaci sannan ya ce, haba Shahida! Me kike son ki fada min?, ai babu abin da zuwana zai kara mata illa ciwo, ba wai ba na son zuwa ba ne, sai dai ina tunani barinta a yayin da na juya baya ta ga mun fito tare da ke zamu koma gida, wannan yanayin shi ne zai zama mafi muni daga ko wanne yanayin a rayuwarta.
Ina addu’ar Allah ya ba ta lafiya, kin ga haka shi kuma Samir yana nan cikin rashin lafiyar sonta yau tsahon wata guda da wasu kwanaki, amma shi an kusa kawo karshen son da yake yi mata, shi ne misalin da nake baki a yanzu, kin ga ba zai yiwu ki dauki Hafida ki kai ta wurinsa ta duba shi ba, matukar dai ba cewa za ta yi tana son sa ba, wannan Kalmar ita ce maganin cutar, kamar yadda ni ma ita kadai za ta maganta wa Hafida ciwonta.
Al’amura ne masu rikitarwa, amma idan kin ce a yi hakan zan aikata saboda bin umurniki. Ta ce, ina da bukatar a yi hakan domin kuwa ina son ta gane cewa ni ba na gaba ta da ita, kuma ban riketa a zuciyata ba. Ina mai yi maka da rantsu idan har da za ka aminta da aurenta, to ni zan iya hakura da kai, hakan kuma ba yana nuna ba na sonka ba, a’a sai dai idan hakan zai ba ta rayuwa mai inganci zan aminta da hakan.
Asadu 33

Exit mobile version