Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (39)

Asadul Muluuk

Na gode wa Ubangijin rana da wata, Allah ya kara wa Annabi daraja,” Ya ce; “Amin.”
Bayan sun yi sallama da maraice daidai lokacin Sallar Magriba, Asadulmuluuk ya ya je wurin mahaifinsa ya gaishe shi, ya kalleshi ya ce; “Kai yau na ganka cikin fara’a ko ka zo min da wani bakon albishir ne?” Asadulmuluuk ya yi murmushi ya sunkuyar da kai. Sarki ya ce; “To dangane da yadda nake ta kokarin ganin ka fidda matar da za ka aura amma har yau na ga shiru, shi ya sa na yanke shawarar nema maka ‘yar abokina Abdul’ilaahi Addumashki, wannan shi ne albishir din da zan yi maka, idan Allah ya mayar da mu gida lafiya, zan hada ka da jama’a ku tafi izuwa Dumashka.
jiya mun zauna da Sarki Abdul’ilaahi Addumashki kan batun ‘yarsa mai suna Suldaanatu kuma ya yi alkawari ya ba ka ita, idan Allah ya mayar da mu gida lafiya za’a fara shirye-shiryen biki, amma kafin haka ya kyautu ka je ka ganta ku fahimci junanku.” Gama fadar haka ke da wuya sai ya ga hawaye ya zuba daga idanunsa sharrr.
Daga ranar da aka haife shi zuwa wannan lokaci, mahaifinsa bai taba ganin ya zubar da hawaye ba, in ba na kukan jarirai ba. Hankalin uban ya tashi, “Yarima fadi abin da yake damun ka in ji, idan na yi ne a yi in kuma na shawara ne to ina tafe da mutane ma su ba ni shawara ta gari.”
Asadulmuluuk ya jima cikin shesshekar kuka ya kasa fadin abin da yake son fada, mahaifinsa ya ce; “Ban san abin da ya sanya kake kuka ba, kuma na fahimci zuciyar ka tana neman ta sarke, shi kuka idan ya zo kuma ba a samu damar yi ba, ya kan zamar wa mutum cuta, ni kuwa a shirye na in yaki dukkan duk abin da zai cutar da kai, jeka ka zauna duk sa’ilin da ka samu sassauci ka zo min da dalilan kukan ka.”
An yi haka daf da lokacin Sallar magriba, aka shiga masallaci aka yi Sallah mahaifinsa bai ga ya fito ba, haka zalika Sallar Isha’i.
Ya aika daya daga cikin masu kula da shi ya je ya ga halin da ya ke ciki, amma ka da ya nuna masa aiko shi aka yi. Da ya isa kofar dakin ya same ta a kulle abin da bai taba gani ba, da ya nutsu sai ya dinga jin sautin kuka sama-sama. Ya juyo zai je ya gaya wa mahaifinsa, sai ya yi kicibis da Zuhairu, a nan yake rada masa halin da ake ciki, kuma ya ce, yanzu ma zai koma ne ya sanar da Sarki.
Zuhairu ya ce; “Kai wane irin sauna ne, wa ya gaya maka ana zuwa a fadawa Sarakuna irin wannan sakon, yanzu yadda yake matukar sonsa, idan ka je ka fada masa ya yanke jiki ya fadi ya mutu fa? Ka jawowa kanka hukuncin kisa, don ba za yarda da duk abin da zaka fada ba, cewa za a yi aiko ka aka yi ka je ka kashe shi.

Yanzu ka je kasanar da Sarkin cewa, ka sa mu kofar a kulle ka yi sallama bai amsa ba, kana zaton ko bacci yake, wala’alla shi Uban ya san abin da yayi masa sai shi ya zo da kansa, ka ga duk abin da ya gani wannan ba ka da aibu”. Ya yi masa godiya suka juyo ya koma wurin Sarki ya fada masa kamar yadda Zuhairu ya tsara masa, Sarki ya yi murmushi ya tashi da kansa ya tafi dakin ya kwankwasa har sau uku, amma bai zo ya bude ba.
Ya kirashi da sunansa na ainihi; “Abdul’azim ni ne mahaifinka Nurussabri Al’akbar ka bude min kofa, na zo ne na ji abin da yake damun ka, ka ga na kasa bacci babu Sakina a tare da ni, sai ya ji sautin kukan na sa yana sake hauhawa.
Saboda gudun kada zuciyarsa ta motsa sai ya juya ya tafi ya ba shi wuri, a wannan dare da Asadulmuluuk da duk wanda ya biyo tawagarsu babu wanda ya runtsa bacci, amma saboda kaifiyya na iya tafiyar da mulki babu wanda ya san abin da yake faruwa daga sauran Sarakunan.
A bangaren gimbiya Badee’atulkhairi kuwa, da shigarta gida ba ta tsaya ko ina ba sai wurin mahaifiyarta, ta ba ta labarin halin da ake ciki tun daga farkon haduwarsu har zuwa wannan lokaci. Mahaifiyarta ta rungume ta ta sumbance ta, ta sa aka kirawo sauran matan Sarki ta ba su wannan kyakkyawan labari, suka yi murna da jin haka, suka yi addu’ar fatan alkahiri. Da dare ya yi na wannan rana sarki ya shigo gida mahaifiyarta ta shiga turakarsa ta ba shi labarin da ‘yarsu ta zo musu da shi.
Sarki ya yi murna ya yi godiya da san barka, ya fada wa mahaifiyarta cewa ga sakona zuwa ga gimbiya, a fada mata na amince da hakan, kuma ina mai goyon bayan al’amarin Allah ya shige mana gaba.” Ita ma mahaifiyarta ta ji dadin wannan karba da sarki ya yi wa lamarin, ta yi godiya ta fita, aka kwana cikin gidan nan ana murna da farin ciki, amma iyakar jama’ar cikin gida ne ke yi.
A can bangaren su Asadulmuluuk sun kwana sun tashi cikin tashin hankali, jamar su Asadulmuluuk ba su san abin da Sarkinsu ya yi wa dansa ba, shi kuma Sarki bai san abin da ke zuciyar dnasa ba. Shin auren ne ba ya so ko kuwa ita wadda aka ce za a ba shi ce baya so, ko kuma wani lamarin ne daban?
Shi kuma Asadulmuluuk yana tsammanin babansa ya samu labarin soyayyarsu ne a boye, don haka da ya zo gabansa ya ga yana fara’a ya yi sauri ya tari numfashinsa da wannan magana, wannan ce ta sa kowa ya zauna cikin rudani da zargin kansa. Sai ya zamto nan bangaren sun kasa bacci don rashin kwanciyar hankali.
Bangaren su gimbiya da iyayenta kuwa suka kwana cikin murna da farin ciki. Kashegari can baya an fito daga Sallar Isha’i labari ya isa wurin gimbiya daga harshen Ummu Nazifah ita kuma ta ji daga Zuhairu, Zuhairu kuma ya ji daga wancanan ka bawa, cewa Asadulmuluuk baya cikin kyawun yanayi, har ma ya kasa fitowa Sallolin Magriba da Isha’i.
Da jin wannan magana Badee’atukhairi ta fita daga hayyacin ta, ta kasa cin abinci duk harkokinta suka tsaya cak, sai kuma jikinta ya fara zafi zazzabi yana hauhawa daga baya kuma sai ciwon kai, aka sanar da mahaifiyara halin da ake ciki, ta zo har dakin ta ji yadda take sumbatu saboda zafin zazzabi, ta sa jakadiya ta kirawo sarki shi ma ya zo aka tambaye ta, ta yi musu bayani har da irin yadda ta fahimci Asadulmuluuk irin yadda yake tsoron mahaifinsa, aka yi kokarin ba ta magani ta sha bacci ya kwashe ta.
Kashegari Sarakuna sun zo za su yi karin kumallo kamar yadda suka saba, Sarki Ainunnasrudden ya makara ana sauraronsa, daga baya ya shigo a fusace yana fada, ya zo kusa da mahaifin Asadulmuluuk yana cewa, ta yaya za ka sanya wa danka tsoronka haka, yaro ya dinga tsoronka kamar kai ka halicce shi, wannan ita ce tarbiyyah Islamiyyah? A’a ko kusa wannan ba ta yi kama da tarbiyyar addinin Musulunci ba, ga ka da kafiya a kan abu idan ka yanke hukunci babu wanda isa ya saka ka janye kamar saukar wahayi, ka zama kamar La Yus’alu amma yaf’alu, babu wanda ya isa yayi maka gyara ko hani akan abin da ka yi hukunci?
To ka yi sauraro, Allah fa shi ne fiyayye mai tanadi ka kiyayi kanka, sannan ya sassauta muryarsa cikin kalamansa yana mai ci gaba da cewa; “Al’akbar ka ji tsoron Allah a cikin al’amarin wadanda Allah ya salladaka a kansu, ka sani mulkin nan a nan duniya muka same shi, kuma nan za mu tafi mu bar shi ko mun ki ko mun so. Saboda me kullum danka ba shi da wani sukuni a rayuwarsa saboda komai yake yi idonka yana kai? wannan dabi’a ce mara kyau. Masu ilmin sanin Allah su ne suke aikata haka, to ina ga jahilai? Ashe su daidai suke aikata komai.
Sannan ya juya ya duba Addumashki ya ce; “Kai ma za ka zama daga cikin wanda zai amsa wa Allah wannan tambaya ya yin da ran mutum daya salwanta a cikin yaran nan guda biyu.”

Exit mobile version