Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (47)

Asadul Muluuk

Asadul muluuk Ya Hadu Da Ibtila’i

Ya sassauta murya ya ce; “Asadulmuluuk tafi ka karasa shirinka za mu kama hanya.” Badee’atulkhairi ta tuna irin kaunar da Asadulmuluuk yake yi mata, amma ta ga ya zo ya wuce ta ko  kallonta bai yi ba balle ma ya saurare ta, saboda biyayya ga mahaifi. Ta kira sunan sa har sau uku ya danyi jim kamar zai tsaya taga ya sake ci gaba da tafiyarsa kamar cewa shi wani kurma ne. Ta yi kamar ta bishi sai ta ga an buda wa babansa wuri zai fita.

Ta zo ta sha gabansa tana kuka ta durkusa tana mai kama kafafunsa tana yi masa magiya cewa; “Ya Abu Abdul’azim ka yi ceton rayukanmu kada ka raba mu da shi, idan ka raba mu kamar ka raba mu ne rayukanmu.”

Abin da ba a taba gani ba kuma ba a taba tsammani ba, sannan mafi girman abin al’ajabi ga duk wanda yake wurin shi ne, hawaye da ya dinga zuba daga idanun Sarki Nurussabri A’akabar kamar ba zai tsaya ba. Ya durkusa kamar yadda ta ke durkushe ya kama hannauwanta ya tashe ta tsaye, ya fidda wani farin kyalle mai kamshi ya share mata hawayenta, ya ce; “ Yata ki yi hakuri, da ina da halin barin sa a nan da ba zan dauke shi ba. Tafiya da shi shi ne mafi alkhairi gare mu baki daya, na yi Imanin idan har na bar shi a nan to sai an samu masu halaka shi, kin ga idan haka ta faru da ni da ke duk mun yi asara, ina sa ran ba da dadewa ba za ki zo kasata a matsayin kin a amaryarsa, na yi alkawarin tsayawa kai da fata wajen ganin kin zama matarsa, tunda mahaifinki ya yi alkawri a kan hakan.

Ki kara hakuri na san rabuwa da masoyi babu dadi.”

An dauki lokaci mai tsaho yana rarrashinta har sai da jama’a suka yi zaton ko ba za a tafi ba, domin duk kan kalaman da yake yi mata babu abin da ya ke zuba daga idanunsa sai hawaye. Asadulmuluuk ya yi tsammanin ko wani abu ne ya ke faruwa, ya dawo don ya ga abin da yake faruwa.

Da ya iso ya ga an gewaye sarki sai ya ga ashe rarrashin Badee’atulkhairi ya ke yi, a nan ransa ya kara yin fari, don ya san dukkan wani zato da yake yi a kan ko ba zai yarda ba, yanzu ta fahimci yadda lamarin yake, ganin haka ya sa ya juya ya koma da baya.

Da sarki ya gama rarrashinta ya tabbatar hankalinta ya dawo jikinta, sai ya sa aka rakata gida, su kuma suka fara hawa dawakin su aka fara tafiya.

Gimbiya Badee’atulkhairi tana kwance bisa cinyar babarta sai aka zo aka ce mata baki fa sun yi gaba, mahaifiyarta ta umarce ta da ta yi azama ta bi su don su yi bankwana da shi.

Kafin a shirya dokinta an yi nisa, don haka ana gama shiryawa ta haye ita kadai ta sakar masa linzami.

Ta na cikin tafiya sai ta tsinkayi wazirin babanta da wani bawa da ake kira Mal’uunu a tsaye, da ta zo kusa da su sai ta tsaya ta tambaye su, ko lafiya ta gansu a nan? Wazirin ya ke amsa mata sun yi mantuwa ne shi ne zai aike shi ya koma gida.

Sai ta wuce nan ta ci gaba da tafiya har ta iske su, da ta ga ta kusance su, sai dan tsaya daga baya ta samu wani bawan gidansu ta umarce shi da ya sanar da Asadulmulluk ta na son magana da shi.

Da aka sanar masa, sai ya nemi iznin mahafinsa, dama a tafiyar mahaifinta shi ne yake daga hannun dama sauran sarakuna suna biye da su, sai kuma ‘ya’yan sarakuna suna biye da su.

Asadulmuluuk ya dawo da baya ya zo in da take suna tafiya a hankalin suna hirar bankwana, an samu kamar rabin sa’a ana tafiya.

Can kawai sai aka ji dokin Asadulmuluuk ya yi wata irin haniniya mai karfi, jama’a suka waigo aka ga ya yi rimi sama Asadulmuluuk ya fado kasa dokin kuma ya fado kansa, shi ma aka ji ya yi kara, ashe bawan nan ta wuce suna tare da wazirin babanta shi ne ya kawo masa hari da wani irin bakin mashi da nufin ya tsire Asadulmuluuk, Allah ya saukaka abin sai mashin ya caki kwankwason dokin shi ne dokin da ya ji zafin shigar mashin ya yi rimi ya fado kan Asadulmuluuk. Nan take dokin ya mutu saboda dafin da yake jikin mashin ya ratsa shi, aka taru nan da nan aka janye shi daga kai, Asadulmuluuk shi ma sumamme aka same shi baya ko motsi, sai ka yanke shawarar komawa cikin gari. Mahaifinsa fadawa sauran Sarakunan ya dauke musu komawa, don haka kowa ya tafi kasarsa.

A nan suka jajanta masa, suka yi masa addu’ar Allaha ya ba wa Asadulmuluuk lafiya. Da aka dawo cikin gari ana duba shi sai aka samu karaya biyu ko wacce kafarsa akwai karaya guda daya, aka kirawo sarkin dori na kasar ya dora shi.

Kashegari da safe aka gurfanar da Mal’uunu gaban Sarki don a tambaye shi, dalilin da ya sa shi aikata haka ko wanda ya sa shi.

A wannan rana Badee’atulkhairi ta halarci fada, kuma shi ne karo na farko da fara zuwa fada don kallon yadda za a yanke hukunci, an jima ana tambayarsa, amma ya ki cewa komai. Ana cikin haka sai ga waziri ya shigo a makare, ya samu an gurfanar da wannan bawa ana tambayarsa, ya yi gaisuwa ya kalli sarki ya ce; “Ranka ya dade wannan mahaukacin wa ya kawo shi nan?”

Sarki ya kalle shi cikin mamaki ya ce; “Au dama ba shi da hankalin?” waziri ya ce; “ Ranka ya dade mai hankali ne zai aikata abin da ya yi? Ai tuntuni ya samu matsala a kansa, don haka ka ga a ko da yaushe ina baya-baya da shi.” Sarki ya ce; “Aje a cigaba da tsare shi kafin a tabbatar da gaskiyar lamarin.

Badee’atulkhairi ta fusata ta mike tsaye ta dubi waziri ta ce; “ Na rantse da Ubangijin mahudar rana da faduwarta sai na yi ajalinka,” Sarki yana kiranta ta juya ba ta ko waigo ta saurare shi ba ta shiga cikin gida.

Wuri ya yi shiru aka rasa wanda zai ce uffan, daga baya Sarki ya ce; “Wannan ai ba abin da za a tsaya ana wani tararrabi ba ne, zafin ciwon abin da ya samu saurayinta ne,” aka ci gaba da fadanci.

Exit mobile version