Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (61)

Asadul Muluuk

Ya ci gaba da cewa, wadda ta raba ki da iyayenki wata aljana ce kawar mahaifiyarki, wadda sun jima suna kawance ba tara da sanin mahaifinki ba, da ta samu cikinku sai ta ta yi wa mahaifiyarku albishir da cewa ai tagwaye za ta haifa, jin haka kuma mahaifiyarku ta yi mata alkawarin in har hakan ta kasance, to za ta ba ta daya daga cikin ‘ya’yan ta tafi da shi yankin aljanu idan ya girma sai ta dawo dashi.

An yi haka kafin a haife ku bayan an haife ku ne aljana ba ta yi shawara da mahaifiyarki ba kawai ta hanke hukuncin dake ki. Laifin aljanar a nan ne da ta yi alkawarin mayar da ke kuma ta ki, laifin mahaifiyarki kuma a sanda za ta haihu na je mata ruwan zamzam na nemi ta yi amfani da shi amma aljanar ta hana ta.

Sunan aljanar Zeenatuzzaman ‘yar wani babban sarkin Musulmin aljanu ce, aikinta ke nan ta rika diban ‘ya’yan mutane tana raba su da iyayensu.

Ita ce ta kawo ki gonakin Nahrusshabbab, sunan wadda ta rike ki a matsayin mahaifiya  Na’arashussa’adaaniyyah ita kuma uwar gidan wani manomi ce, shi kuma manomin sunansa Muslihuzzahree, kin samu horo a wurin a wurin Abdussamad cikin wata katafariyar fada mai dinbin tarihi ta sarki da ake kira Suldanil’usfuur, shi kuma Suldanil’usfuur shi haifi mahaifina, ni jikansa ne sunana Abdurrabbi.

Sunan mahaifinki sarki Nuussabri al’akbar kuna zaune Tanzeemussalam, akwai babban wanku ana kiransa Suldan, shi kuma abokin haihuwarki ana yi masa lakabi da Asadulmuluuk, amma sunansa na hakika shi ne Abdul’azeem, duk wanda ya ganiki ya gan shi sai dai kawai a ce ke mace ce shi namiji ne, amma idan kika yi rawani baku da banbanci.

Bayan ya kammala yi mata bayani sai ya mike tsaye ya ce biyo mu je ki gani, shige gaba tana binsa a baya hara suka shiga wani katafaren daki mai wadansu irin fitilu masu haske.

Ta gay a sanya hannu ya yaye wani farin yanki sai wani bango a jere takobba iri-iri, jikin bangon an daje shi dardumai na zinare wurin yana kamshin turaren da bata taba jin irinsa ba, sai ya fara yi mata bayanin takobban kamar haka.

“ Wadan nan kaya da kike gani kayan yaki ne da wasu bayin Allah suka yi amfani da su daga shahen mutane da aljanu, wadan da al’ummar zamunna ba za su manta da su.”

An nuna mata takobin Yarima Anwar dan sarki Nawwas al’imsha, wadda take dauke da sirrin ayatulkursiyyu, sannan ta ga zoben Gimbiya Sanawiyyatul’azmanati na zinare, mai dauke da sirrin Yaseen, daga gefe kuma ga takalmin hadimarta nan Bintu ahsanussanawiyya, ta ga takobin daukar  fansa wadda ke dauke da sirrin Hasbunallahu.

Haka zalika ta ga takobin Bintu Nuzhatunnashaar wadda ke dauke da sirrin Asma’ullahilhusna, da sauran kayayyakin tarihi. Bayan an kammala nuna mata wadan nan kayayyaki sai aka jagorance ta zuwa wani karamin daki daban aka nunamata wani takobi da ta ga an rubuta sunan Asadulmuluuk, to a nan sai ta yi tambaya ta ce, “ Ka ce sunan abokin haihuwata ne mai irin wannan sunan, yaya aka yi kuma na ga wani mai suna irinsa.”

Ya ce ai wannan takobin tasa ce, shi ma nan gaba za mu gayyace shi ya zo nan domin ya karba. Wannan shi ne karo na farko da yaro mai kankantar  shekaru kamar sa zai karbi takobi a nan. Suka wuce zuwa daki na gaba ita kuma aka dauko wani zoben tagulla ya mika mata, ya ce, bisa umarni, wannan zoben za ki iya ba wa masoyinki wanda za ki aura,” wadan nan su ne abubuwan da aka umar ce ni na baki, idan kin so ki sake kwana a nan saboda gajiya, idan kin so kuma kya iya tafiya don komawa gida.

Ta ce, zan zauna na huta tsahon kwanaki biyu saboda ban jima da dawowa daga wata tafiya ba, dama ina neman yadda za a yi na samu hutu, don haka zan tsaya sannan idan dare yayi zan zo da jama’ata su gaishe ka don su ma su karu da wasu abubuwa na tarihi. Saboda su ma dakaru ne da muke son su zama wasu mayaka nan gaba.

Bayan ta kammala zamanta na kwana biyu suka kama hanyar komawa gida, suna tafiya ita kuwa babu abin da yake cikin zuciyarta sai maganar aljana Zeenatuzzaman abin yana damunta a zuciyarta.

Da komawarsu gida ta fara shirye-shiryen zuwa gidan iyayen da suka rike ta tare da fushin yadda za ta hadu da aljana Zeenatuzzaman, da kuma tunanin yadda za ta sadu da dan uwanta, da kuma tunanin yadda za ta kai masa dauki game da tsautsayin da zai same shi.

Tunanin ya yi yawa a zuciyarta, ta rasa da wanda za ta yi shawara da shi domin al’amari ne na sirri ne da ya shafe ta ita kadai. Daga baya dai ta yanke shawarar yin tafiya zuwa can yankin, amma dai jama’ar garin da ke mulka sun fahimci tana cikin wani hali na rashin jin dadi. A duk lokacin da ta fito fada ba ta iya dadewa ana fadanci kamar da, sannan kuma babu walwala a tare da ita, haka zalika, kullum tana zama cikin yawan kawaici da rashin kula da kanta wajen kwalliya, bayan an san ta da kwalliya da sakin fuska.

Mako na biyu daga cikin makonnin da ta dawo, ta tara ‘yan majalisara ta shaida masu cewa, idan Allah ya kaimu karshen makon gobe za ta yi tafiya domin ziyartar iyayenta.

Exit mobile version