Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (63)

Asadul Muluuk

Daga nan sai mijina ya ce a sakamakon wannan mafarki da kike yi, idan Allah ya kai mu ranar laraba zai kai fara zuwa koyon yaki, ta kan iya yiwuwa ki zama abin alfahari nan gaba.” Cikin murna da farin ciki kika ce (Abuuya) yaki kuma! na takobi da mashi, ko kuwa harbi da kibau.?”

Yayi murmushi ya ce; kin shirya ne.?” kika yi dariya kika ce; “Ai ni yarinya ce daga nan kuma sai wani tunani ya zo miki kika tambaye mu cewa, mu baki labari, shin ina wata kawarki da kuke zuwa makaranta kuna ‘yan yara,? na amsa miki, ai sun koma wata alkarya mai nisan zango daga wannan alkarya tamu.

kika ce, kash kinga da a ce mu mawadata ne da mun hau rakuma mun kai musu ziyara, ke ma a wannan lokaci sai hawaye ya zubo daga idanunki, kika sanya hannu kika share, kika dauki akushin abincinki kika koma dakinki cikin sanyin jiki. Amma nasan ba zaki iya tuna duk irin wadannan abubuwa ba, kinji kadan daga muhimman abubuwan da suka faru a rayuwarki ta kuruciya.

Hadiyatul’aini ta cira hawaye na zuba daga idanunta ta numfasa ta ce, dama ni  jikina yana bani kamar cewa ba na tare da iyayena, sai dai a yadda tunanina yake bani, ina zaton ko ina kusa da mahaifana ne ashe abin ya saba da tunanina. Yanzu abin da ya dace a nan shi ne za mu tattara mu mu koma can Manzilatussurayya ne, domin na fahimci bayyana wannan sirrin zai iya sanya ku cikin wani hadari na daban.

Amma idan da za ku iya jure wani abu da an samu salama, shi ne, yadda kuka iya rike wannan sirrin nata har na tsawon shekaru ya kamata ku ci gaba da rikewa har lokacin da Allah zai dawo da ita, a zuwa na farko kenan da za ta yi na ziyarat a gadon mulki. Shin akwai wani lokaci da ta diba na cewar za ta zo wurina?

“ Eh, ta yi alkawarin ranar da kika cika shekara guda bisa gadon mulki za ta zo ziyararki,” in ji Muslihuzzahri. Hamdiyatul’aini ta ce na rantse da Ubangijin mahudar rana da faduwarta idan muka yi arba da ita sai hallaka ta, kuma ni mai samun nasara a kanta ne cikin yardar Allah. Na’araashussa’adaniyya ta ce, ‘ya ta yakarta ba shi ne abin da zai fitar da mu daga halin da muke ciki ba, addu’a ita za ta fitar da mu.

Hamdiyatul’aini ta ce, haka ne za mu yi addu’ar kuma za mu yake ta, domin idan fa hakan aka yi ba, to fa ni da komawa ga iyayena har abada, Ummi ta yaya wadda ta yi alkawarin idan nay i wayo za ta mayar da ni ga iyayena amma gashi har na kai matsayin sarauniya har yanzu ba ta zo kana maganar ba? kin san wannan akwai wani gilli a zuciyarta.

Tashi tsaye a yake ta ta ko wace fuska ita ce mafita, idan ba haka ba a irin hatsabibancinsu na aljanu sai sai wata rana ta yi binciken gano wannan sirrin duk ta hallaka mu. Wannan aiki ne da za ku bar shi a hannuna, za a ci gaba da rokon Allah har sai Allah ya sallada mu a kanta. Jibi idan Allah ya kaimu ku shirya kayanku gaba daya mu bar wannan alkaryar mu koma can Manzila, kun ga idan ta zo ta tambaye ku dalilin yin haka sai ku fada mata cewa ba zaku iya rayuwa ba tare da nib a don haka ne kuka dawo kusa da ni, hakan zai sake ba ta kwarin gwiwa domin ta san a alkaryar babu wanda ya san ku balle ya san halin da da muke ci.

Suka amince da hakan, da lokaci ya yi suka shirya gaba dayan su suka koma konakin Manzila, aka ci gaba da gudanar da harkar mulki cikin adalci. Wata rana ta tara manyan garin suka zauna domin su tattauna. Bayan kowa ya hallara ta yi musu bayani cewa tana son a tattara mata malaman kasar domin su fara yi mata addu’a kan wata bukatar ta ta daban.

Tun daga wannan rana kusan ko da yaushe sai ta yi mafarkin wai gata cikin wata kasa mani’imciya tana tare da iyayenta. Cikin mako guda daga makonnin komawarsu neiyayen suka yi kiranta akan maganar aure, “ To yanzu haka za ki zauna  ba tare da kin yi aure ba, yin hakan ai ya sabawa addini kina a matsayin sarauniya,” in ji, Muslihuzzahri.

Hamdiyatul’aini ta ce, kun san hakan na daga cikin makasudin zuwana wurinku, amma yanzu wannan mas’alar ta zo ta sha gabana. Abin da ya tsorata ni har tafi wurinku don ku gaya min gaskiya shi ne, na kasance tun a wata na biyu daga cikin watannin nan takwas da na yi a kan mulki, fada ta tana cika kakil da jama’a, amma abin mamakin shi ne, ba zaku ga mata da kananan yara ba, daga samari sai matasa da dattawa.

Da na tsawaita bincike saia aka gano min cewa, kashi casa’in daga cikin kashi dari na masu halartar fada duk suna zuwa ne domin sun kalle ni a matsayin kyakkyawa, al’ummata sun rudu da da kyawuna, yayin da ni kuma nake shagala da kokarin wanzar da adalci yayin da hukunci ya zo gabana.

To inda babban kalubalen yake shi ne, idona ya taba afkawa kan wani saurayi ma’abocin kwarjini da nutsuwa, wanda na kare tunanina wajen gano mai yake kawo shi fada tare da sawa a yi min bincike, sai bayanai suka nuna ai shi yana zuwa ne kawai domin ya koyi salon tafiyar da mulki, sai dai abin tausayi iyayensa manoma kuma makiyaya. Sha’awar sha’anin mulki ta mamaye zuciyarsa a lokacin da son sa ke kokarin mamayar zuciyata. Na samu zama da masu ba ni shawara kan ko na aure shi?

Mafi rinjayensu suka nuna rashin amincewarsu, a cewarsu me ya sa ina wannan matsayi zan auri wanda ba kowa ba? amma daga irin amsar da nake ba sui ta ce, labarinku da na ba su cewa iyayena kamar na sa iyayen ne, daya daga cikin su ya tari numfashina ya ce binken da ya yi gudanarwa ya bayyana masa ni ‘yar sarauta ce, bayan wannan an gayyace ni birnin Bagdad in da na samu labari makamancin nasa, to wannan dalilin ne ya sanya na zo gareku. Ina gani rannan hadimaina suka kori saurayin nan daga fada, amma na kasa cewa komai duk na san ba shi da wani laifi.

Abin da tsoro nan gaba shi ne kada jama’ata su kori iyayensa daga wannan alkarya, yanzu ne nake gane cewa masarauta cike take da hassada da masu kyashi. Muslihuzzahri ya ce wannan shi ne kusukuren da kika yi a wannan masarauta, don haka ki gaggauta yin binciken nemo wannan yaro don a bashi hakuri, idan kuma kina sonsa, to kada a bayyana masa har sai kin samu ganawa da iyayenki kin yi shawara da su, in sun amince to sai ki aure shi, in an samu akasi sai ki hakura.

Hamdiyatul’aini ta ce, zan aikata hakan in Allah ya so, amma yanzu babu komai a gabana illa ganin na kawar da waccan bakar azzalumar aljanar, kuma sai na hallaka ta da iznin Allah, gobe kuwa zan aika cikin sirrin a binciko min halin da suke ciki.

Exit mobile version