Manzannin sarauniya Hamdiyatul’aini suka zauna zaman jiran dawowarsa domin isar da sakonta, jakadiya ta shiga cikin gidan suka gaisa da mahaifiyarsa da kakarsa. Kakarsa ta tambayi jakadiya ranki ya dade ki bani labari shin me muka yi wa sarauniya har take neman wannan da namu, yalla ko dai zaman fadar da yake zuwa kallon hukunci shi ne mulki ya motsa aka ce ya yi laifi? A karo na farko kin ga irin yadda attajirai suka tsangwame mu tare da cewa ba mu san abin da muka yi musu ba,? ina mai yi miki rantsuwa ubangijin mahudar rana da faduwarta ba mu san wani laifi da muka yi musu ba.
Jakadiya ta ce, ni dai ba kowa b ace illa jakadiya, sarauniya ta aiko ni tare da ‘yan rakiyata domin nemo ku duk inda kuke, sanin abin da kuka yi na laifi ko akasin haka ban sani ba, abinda ya inganta a sakon da aka aiko ni shi ne, na nemo ku duk inda nake in kuma na samu inda kuke to kada na koma sai da shi, amma dai bisa la’akari da abokan rakiyata na san ba aike ne na fushi ba, domin da aike ne na fushi da an hado ni da fusatattun fadawa.
Ana cikin haka sai gashi sun shigo da mahaifinsa sun yi sallama yana dauke da kayan aikin gona. “Kash amma duk nag a ya canja,” in ji jakadiya. Ya dube ya ce, haba baiwar Allah me na yi miki kike ta bibiyata, a baya da ke aka kama ni aka yi min bulala cikin dare gami da umarnin kada a sake gani na a wancananka alkarya, na tattaro iyayena muka baro muku kasarku, kuma mun dawo nan kina kara bibiyata. Yanzu me kike bukata a garemu, kuna so nan din ma mu bari mu koma wata kasar.?
Ina son ki sani kasar Allah na da yawa kuma babu wanda ya isa ya hana bayin Allah rayuwa a doron kasa, ku bari idan lokacin barinmu duniya yayi za a zo a gaya muku jana’iza. Jakadiya ta mike tsaye ta je ta durkusa ta kama kafafunsa tana cewa, don Allah dan saurayi ka yi min rai, na san ban kyauta maka ba, na yi abu cikin rashin sani amma ina neman afuwarka.
Iyayen suka dube ta cikin mamaki “ Ke ko dai ke ba jakadiyar sarauniya bace,” in ji kakarsa. Jakadiya ta ce, wallahi jakadiya ce daga fadar sarauniya Hamdiyatul’aini, amma ina son ku rarrashe shi ina mai yi muku rantsuwa idan har sarauniya ta ji cewa da ni aka yi masa wancan rashin kyautawar to babu shakka zan dandana kudata, domin a halin yanzu ma tana kan binciken wadan da suka aikata hakan. Amma dai yanzu fatana a ce mu tafi tare kamar yadda sarauniya ta yi umarni.
Da kakan ya ji haka sai ya ce, ke jakadiya idan har za ki aminta da abinda zan fada yanzu to zai je har inda kuke, in kuma ba zaki aminta da hakan ba to ba zai je ba. sharadi a nan shi ne, ku koma yau shi kuma idan Allah ya nuna gobe za su taho da abokansa, ni kuwa mai cika muku alkawari ne kan haka kuma na lamunce. Domin babu wani dalili da zai sa mu baku shi ba mu san abin da ke cikin zukatanku ba.
Da jakadiya ta ji kalaman kakansa sai ta amince, suka yi bankwana ta fito ta yi wa ‘yan rakiyarta bayani daga nan suka kama hanyar komawa. Da zuwansu jakadiya ba ta zame ko ina ba sai gaban sarauniya, ta bayyana mata duk abinda ya faru tun daga lokacin zuwansu har lokacin da suka baro garin.
“ Dai dai wane lokaci suka yi alkawarin isowa nan,” in ji sarauniya Hamdiyatul’aini. Jakadiya ta ce, ina kyautata zaton za su shigo ne bayan kammala zaman fada. Sarauniya ta yi godiya da san barka ta sallame ta. kashe gari ana tsakiyar fadanci sai gashi ya zo shi da abokinsa suka samu wuri daya can suka zauna inda ba kowa ne zai gane su ba. bayan an gama zaman fada an yi addu’a kafin sarauniya ta tashi sai ya fadawa wani bafade cewa a sanar da sarauniya ta yi baki.
Bafaden ya kalle shi kallon wulakanci yace, kamar ku ku ce kuna son magana da sarauniya, don dai kawai kun ji ana cewa tana da adalci kawai sai ku zo ku ce kuna da magana da ita? Ku tashi daga nan ko na mangare ku shakiyyan yara, kalle ku ‘yan kananan yara da ku sai tsaurin ido.
Yayi masu korar kare suka koma daga can gefen gidan sarauniya suka samu wuri zauna, da lokacin Sallar azuhur ya yi suka shiga masallaci aka yi Sallah da su suka koma wurin da suka fara zama suka suka ci gaba sauraron abin da zai biyo baya.
Can zuwa wani lokaci sai ga wata mata nan ta fito daga ciki, sai da suka bari ta dan yisa da gidan sarauniya suka bi ta suka yi mata magana, bayan sun gaisa suka yi mata bayanain abinda ke tare da su. Ta ce to ai hirarku a ke ta yi a cikin gida, ku da ake neman ku tun safe? Ai tura masu taren ku can bayan gari idan kun zo su taho daku, “ Kai lale-lale marhaba ahlan wasahlan bikum, yau Allah ya kaddara zan karvi goron albishir, ku biyo ni mu je,” in jita.
Ta wuce gaba suna binta a baya har suka isa kofar gidan, fadawa suka taso ciki har da wanda yak ore su, “ Kai wadan nan ina za ki da su,? In ji fadawa, ta yi murmushi ta ce ai wadan nan fararen baki ne, ku dai ku jira ni har nay i musu iso. Bata ajiye su a ko ina ba sai a azure na karshe. “ To ku jira ni ina zuwa,” in ji ta. bayan tafiyarta sai wannan ya kalli wannan, wannan ya kalli wannan.
Ko da isarta ga sarauniya sai ta fadi ta yi gaisuwa ta ce, ranki ya dade albishirinki, na kawo miki bakonki yana nan a azure na karshe shi da abokinsa. Sarauniya tana kishingide ta tashi zaune ta ce jakadiya ta biyu ba a wasa da jaanibin so, ki bani labarin gaskiya ban da zolaya. Jakadiya ta biyu ta ce, Allah ya baki nasara ai yanzun ba lokacin wasa ba ne idan kin yi izni sai a kai su in da kika yi umar ni ko ina ne, amma dai magana ingantacciya suna nan suna jira.
Sai ta yi umarni da akai su babban masaukin da ta ke ganawa da manyan mutane, aka kaimusu duk abinda ake saukar ko wane bako da shi. A nan ne fa suka fara tunanin wani daban da yake zuciyarsu da farko. Daf da lokacin Sallar la’asar sarauniya ta aiko aka sake sauya musu wurin zama inda za ta zo domin ganawa da su, nan ma suka sake cika da mamaki, ya kalli abokinsa ya ce, wannan sarauniyar fa duk tana yi mana haka ne saboda labarin da ta samu na cewar an kore mu daga kasar nan an ci zarafinmu, shi ne ta sa aka nemo ni domin ta rarrashe mu, ka san ba’a tava samun mai mulki mace dake da adalci kamarta ba. abokinsa ya ce, kai amma in dai haka ne a’ummar alkaryar nan suna jin dadi.