Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk (66)

Asadul Muluuk

Nafsuzzakiyya ya ce, ain i ya kamata na yi godiya, domin zama cikin wannan ni’imtacciyar alkarya babban abin alfahari ne ga duk wanda ya dace da hakan. Amma dai ranki ya dade ina neman alfarmarki, don Allah idan mun dawo a mayar da mu gidanmu na farko da muka fara zama.

“ Bawan Allah shi ana yi masa kallon so da kauna shi kuma yana tunanin wani tsohon gidansu,” wabnnan tunani ne sarauniya ke yi a zuciyarta. Daga baya ta yi ajiyar zuciya ta ce, na ji sunanka da na abokinka tun da farko, saura ka bani labarinka da labarin ahalinku. Nafsuzzakiyya ya ce, an hane ni da bayyana tarihin kaina balle na ahalinmu, akasin haka kuma zai iya jefa rayuwata cikin fushin Allah, domin umarni ne daga mahaifana gami da alkawari kan tabbatar da hakan daga gareni.

Ahmadussaafee ya kalle shi cikin mamaki da hanzari ya ce, ka manta a gaban sarauniya kake, me ya sa ba za ka fada mata abin da ta tambaye ka ba? nafsuzzakiyya ya dube shi ya ce, na bayyana mata abin da iyayena suka hane ni, ita na kaucewa fushinta, idan na afka fushin iyayena ta yaya zan kauce wa afkawa cikin ukubar Allah? Ita fa an halicce ta ne kamar yadda aka halicce mu.

Sarauniya ta ce, shin akwai wani hadari dake tattare da da tarihinku ne, yalla ko dai wasu dalilai ne da suka shafi iyayenka,? Amma dai ko menene na yi maka uzurin hakan, yanzu dai bari na ci gaba da tambaya ta gaba, shin kafin a kawo lokacin da wasu suka kore ku daga wannan alkarya, jama’a suna zuwa fada su cika domin sauraron fadanci, kuma labarai suna iske ni cewa wasu na zuwa ne domin su ganni kawai wasu kuma domin su ji muryata da dai sauran wasu dalilai marasa tushe, shi kai kuma me yake kawo ka fada ka zauna har sai an tashi.?

Ya ce, ba zan iya fadar dalilan da suke kai ni fad aba, domin suna daga cikin abubuwan da idan na fade su kamar na bayyana siirin da aka hane ni da bayyanawa ne. ranki ya dade ayi min afuwa har na nemo izni, idan kuma an hanani umarni a gida sai dai a yi hakuri.

Sarauniya Hamdiyatul’aini ta ce, gaskiya iyayenka sun yi dacen haihuwar da mai biyayya, samun kamarka ba karamar nasara ba ce. Abu na gaba zan gaya maka idan mun dawo daga Sallar la’asar, yanzu kuwa mu je mu yi Sallah, idan mun dawo sai na habarta maka.

Bayan sun fita Sallah, sarauniya tana zaune Shaziyah ta shigo ta yi gaisuwa cikin rawar jiki ta ce, Allah ya baki nasara akwai babban al’amari cikin sha’anin yaron nan da kika gayyato, kakansa na biyar shi ne sarkin da a yanzu kike rike takobinsa ta yaki, sunansa Abdul’ilahi Al’ansarie. Shi ne sarkin da ba’a taba samun sarkin da ya gudanar da mulkin adalci kamarsa ba, yayi shahada a wani hari da wasu wabilun Majuus suka kawo a yayin da yake dawowa daga jana’izar amininsa.

Shi kuma wannan yaron sunansa  Muhammadu na fsuzzakiyya dan Salihul’ambari dan Mahbubil’islah, dan Sarki Jalaluddeen al’ansarie, dan Hashimus sa’adee, dan Amiru Asshahidee, dan Abdul’ilahil’ansarie abin ba da fansa da takobin Safwaanassafee mai dauke da sirrin Ayayul’muawwataini. Na san ba zai yarda ya fada miki ba, domin mahaifinsa a wancan lokaci da aka kashe kakansa ana kokarin yi masa adin sarauta cikin dare a sirri ya fita da iayalinsa suka gudu saboda gudun mulki, bai dawo wannan alkarya ba sai da aka yi sarakuna bayar kafin ke, da suka ji labarin an yi sabuwar sarauniya ce suka dawo kasar nan.

Cikin al’ajabi sarauniya ta ce, wannan tarihin da kike ba ni kamar ya faru ne tun kafin haihuwar Nafsuzzakiyya ko? Ina nufin ni ma zamanin ba a haife ni ba, amma ta yaya kika gane shi, sannan da wace alama kika gane shi, kuma me ya alamta miki hakan bayan dadai baki taba ganisa ba sai yau?

Shaziyah ta ce, na kasance ni ce mai hidima ga uwar gidan kakansa wancan sarkin, zoben da a yanzu yake hannunsa zobe ne na danyar zinariya, ko da yake na san baki lura da shi ba.

Sarauniya ta ce, tun kallon farko da na yi wa hannunsa ya fahimci haka bai kara bayyana shi a fili ba, amma dai na sani ko ba yanzu b azan sake ganinsa, idan kuwa har ya aminta da soyayyata lallai zan raba shi da ita, saboda ai ba halal ba ne namiji yayi ado da kayan mata.

Gaskiya Shaziyah kin zo da babban al’amari na gode miki, yanzu dai mu je mu yi Sallah mu dawo. Bayan sun dawo daga Sallah suka samu Nafsuzzakiyya shi kadai a zaune, sarauniya ta tambaye shi, ina abokin naka, ya ce, mun samu wani bawan Allah yana wa’azi a Masallaci don haka ya ce zai jira ya saurari karatu kafi idan fito sai mu tafi.

Sarauniya Hamdiyatul’aini ta ce, na bukaci ka fada min tarihinka amma abin ya gagara, ko da yake kana biyayya ga nagabatanka hakan kuma daidai ne. Amma a iya sanina, idan fadi kadan daga cikin salsalarka zaka fada min wani abu daga cikin tarihin rayuwarka wanda bai shafi iyayenka ba.

Nafsuzzakiyya ya ce, Allah ya baki nasara me ya sa kika damu da sanin ko ni waye cikin tarihin rayuwata? Sarauniya ta ce, saboda ina so na san wanda nake tare da shi, sannan wanda nake burin..sai ta dubi Shaziyah ta ce, ki je waje har sai na neme ki, Shaziyah ta tashi ta fita.

Sarauniya tana daga wurin da take ta ce, ban karasa fadar abin da ke zuciyata ba, amma zan fada maka, shin kai ne Muhammadun nafsuzzakiyya dan Salihul’ambari dan Mahbubil’islah, dan Sarki Jalaluddeen al’ansarie, dan Hashimus sa’adee, dan Amiru Asshahidee, dan Abdul’ilahil’ansarie abin ba da fansa da takobin Safwaanassafee mai dauke da sirrin Ayayul’muawwataini.?

Nafsuzzakiyya ya mike tsaye cikin mamaki ya ce, ke ce gimbiya Nasirah ‘yar sarkin Ni’matullahi,? Sarauniya ta ce wacece hakan ban santa ba. ya sake cewa ko kece sarauniya Islahatul’adlasie? Sarauniya ta ce ban da yau ban taba sunaye masu kama da irin wadanda kake ambata ba. “ Allah ya baki nasara meye makasudin zuwana nan?,”

Sarauniya ta kike tsaye ta ce kai jinin sarauta ne, amma ina son na bayyana maka cewa na kaunace ka tun kafin na san kai dan sarauta ne. ya ce, “ Ai shi ambaton kamar soyayya abu ne mai sauki, amma karbar soyayyar wanda ya furta shi ne abin da ke wahalar sani, ga wanda ya ambata.”

Sarauniya ta tashi daga in da take ta koma tana fuskantar taga cikin kalamanta na soyayya tana mai cewa, igiya ta yi kadan wajen daure miliyoyin kalaman da na zo da su don bayyana maka, sasarin kuma da aka daure kalaman karfin so da kaunarka ya sa sun gaza daurewa ya katse, sai ta waigo ta yaye mayafin kanta iya fuskarta ta bayyana ta ce, ba magana nake yi a matsayina na sarauniya ba, so baya kwankwasa kofa, ba ruwansa da attajiri, basarake ko wani mai mulki ko gwarzon jarumi, wanda duk ya riske shi sai dai ya taka sannu.

Samunka a rayuwata shi ne abin dubawa a zuciyata, akasin haka kuwa sai dai hakuri wanda ya zama dole ba don ana so ba.” “ Ni ba dan sarauta ba ne,” in ji shi. ta ce kada ka boye min ka haka ko akasin haka ina sonka kuma b azan janye ba sai in har kai ne baka son hakan to sai na hakura, ya nzu dai sauraron amsarka nake yi.

Exit mobile version