Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk 80

Asadul Muluuk

Safina ta dube shi ta ce, kada hankalinka ya tashi zan mayar da kai har inda aka umarce ni madamar ina raye, ka shirya za mu ci gaba da tafiya kamar yadda ka bukata. Suka ci gaba da tafiya, ba su jima da tashi ba suka sake samun wata katafariyar alkaryar Larabawa masu launin jiki fatsi-fatsi wadda wata dattijuwar sarauniya ke mulkarsu Sarauniya Saleemah, “ Yawwa, Allah ya kawo mu wata kasar Larabawa ka ga wala’alla ma mu sake samun wasu da suka san labarin kasarku daga nan mun sake samun saukin tafiya,” in ji Safina.

Asadul muluuk ya ce, haba Safina, me kuma ya hada mu da sake neman wasu bayanai bayan an hakikance kin san hanyar kasarmu? Safina ki ji tsoron Allah kada ki bari Shaidan ya kawata miki abin da zai kai ki ga nadama. Safina ta ce Asadu “Ya Asadu, me ya sa ba ka son kyautatawa Musulmi zato? daga nan bai sake cewa komai ba.

Sun shigo cikin alkaryar ana tsananin sanyi, mutanen kasar har ba sa iya fita sai da kayan sanyi, daf da lokacin Sallar Juma’a suka shiga garin, Asadu ya yi azamar yin alwala ya shiga babban Masallacin garin aka yi Sallah da shi. Ko da zuwa wurin da Safina ta ajiye shi, wanda kuma nan ne muhallin da za su hadu domin ci gaba da tafiya, sai ya neme ta ya rasa, ya yi iya kokarin da zai yi na ganin ya same ta ya rasa, domin jama’a ce bila adadin, an fito ana cin kasuwar bayan juma’a.

To a al’adar mutane kasar, duk ranar Juma’a kasuwar garin ke ci, al’ummomi suna zuwa daga ko ina na makwaftan alkaryar, don haka take matukar cika. Da ya gaji ya samu wuri ya zauna kafin ka ce wani abu bacci ya kwashi shi, sai ya tada kai da wannan jaka ta kayan sawarsa. Yana cikin wannan hali na bacci, sai ga masu gyaran hanya suna umartar mutane da su kauce sarauniya ta dawo daga masallaci za ta koma gida. Saka ganshi kwance daga can gefe, suna mamakin yadda kayan jikinsa suke marasa nauyi, suka zagaye shi, daga nan suka fara takaddama, wasu daga cikinsu suka ce “ Kai wannan yaron daga ina yake haka, mu dai ba mu taba ganin irin wannan launin jikin ba, abin da ya fi kawai mu tashe shi mu kai shi ga sarauniya,” Sashinsu kuma suka ce, “ Tab! ku tashi shi amma babu hannuna a ciki, idan kuka taso aljani fa, kuna ganin abu kamar ba mutum ba? Suna cikin haka sai ga shugabanninsu, da zuwa suka gani suka ce ku tashe shi, ashe dama nan wurin da ta ajiye shi kasuwar bayi ce.

Kafin a kai ga tashinsa sai ga Safina cikin wasu kayan kwalliya da ko sarauniyarsu ba su taba ganin ta sanya irinsu ba ga kwarjini, ta tutture su ta ce, me kuke nufi da bawana, wannan malalacin bawan da bai da dabi’a sai bacci, kuna son ku saya ne? Idan kuna so ku zambar Dirhami dubu biyar, nan da nan aka aika wurin sarauniya da gamsassun bayanai ta bayar da kudin. Nan take aka rubuta takarda ta sanya hannu ta bar shi a nan kwance yana bacci ta yi tafiyarta. Babbansu ya ce ku tashi ai ya zama bawanmu, kowa ya yi cirko-cirko ana tsoron kada a tashe shi wani abu mara kyau ya biyo baya, babban ya sauko daga doki ya tashi a hankali. Koda farkawarsa ya ga an zagaye shi, ya yi tasbihi, sannan ya ce, “ ‘Yan uwa lafiya dai? sai babban ya yi masa bayani ya kuma nuna masa takarda, don haka suna umartarsa da ya wuce gaba zuwa wurin sarauniya.

Asadulmuluuk ya tashi ya kade kurarar dake jikinsa ya wuce gaba suka bi shi a baya har suka isa ga sarauniya, tana zaune bisa darduma a kishingide, ko da ganinsa yana isowa sai ta tashi zaune. Aka zaunar da shi da irin kalaman da suke yi gaban sarauniya. Sarauniya ta kalle shi cikin girmamawa da tausayi ta ce, kai yaro ta yaya aka yi ka fada cikin kangin bauta ga ka dan karami haka, shin an ci garinku da yaki ne ko kuwa yaya lamarin yake? Asadulmuluuk ya dan yi jim, kamar dai ba zai iya bayar da amsar ba, wani babban bafade ya fidda bulala ya fada cikin tsawa, “Kai lalataccen yaro ba za ka yi magana ba?” Sarauniya ta mike tsaye ta dakawa bafaden tsawa, ta ce daga yau zuwa ranar da zai bar wannan alkarya kada wanda ya sake yi masa tsawa.

Sannan kuma ga doka zan kafa, daga yau kada wanda ya sake kiransa bawa, daga yanzu sunansa dan sarauniya, kuma da shi ‘ya’yana duk daya na dauke su a wajena. Sannan ta sassuta murya ta kalle shi ta ce, yaro ya sunanka? Asadulmuluuk ya rusuna ya ce, Allah ya baki nasara sunana Abdul’azeem, amma ana yi min lakani da Asadulmuluuk.” Sarauniya ta ce, to na ji sunanka na gode, sauran labari kuma sai mun koma gida, ta dubi mai bayar da masaukin baki ta ce a nema masa doki da zai hau

wanda ba mai gardama ba, idan kuma ya hau dokin ya yi masa rashin ladabi to kai zan ladaftar. Sannan a karbi dukkan kayansa na sawa a wanke su, a kwashe dukkan kayan da suke cikin dakin gimbiya Hayaatunnufuuss a sake fasalin dakin yau din nan ya kwana a cikin dakin cikin aminci, ina son wannan umarni ya fara aiki yanzun nan. Sannan ta ba da umarnin a je a kawo wadda ta sayar da shi ta yi mata tambayoyi. Tana kammala bayananta, aka tashi mutum uku suka koma gida suka kammala dukkan ayyukan kafin sarauniya ta koma gida an kammala gyaran dakin, an zuba duka abin da ya dace a zuba a ciki. Tun daga nan ne wasu daga cikin jama’arta suke ta guna-guni suna cewa, an ya kuwa Sarauniya ba so take ta aure shi ba.? Wasu kuma na cewa, su a ganinsu so take ta aura masa gimbiya Hayaatunnufuuss. ‘Yan aiki suka dawo suka ce sun neme ta ba su same ta ba.

Exit mobile version