Rabiu Ali Indabawa" />

Asadul Muluuk 94

Asadul Muluuk

Asadulmuluuk ya ce, ni fa ban fahimci abin da kake nufi ba, yanzu babu yadda za a yi wani bako ya shigo cikin wannan alkaryar sai iznin wani abu da ban? Bafaden nan ya yi sauri ya rufe bakin Asadulmuluuk ya ce ka yi shiru karshenta yanzu wasu daga cikin aljanunsa suna yawo idan suka ji abin da muke fada za mu shiga cikin tashin hankali, domin daga ni har kai za a iya hallaka mu baki daya.

Asadulmuluuk ya yi kasa-kasa da muryarsa ya ce, shi kuma dodon kamar yaya kamanninsa suke? Bafade ya ce, haba dan saurayi waye zai iya tsayawa ya kalli suffar dodo, sai dai kawai idan ya fito za ka ga hayaki na fita ko ta ina daga jikinsa, sannan za ka ji gari duk ya dauki rugugi da hayaniya, tsuntsaye da dabbobi duk suna shiga cikin dimuwa, hankalin jama’a ya kan tashi har sai ya koma muhallinsa.

” Ina ne muhallin nasa? In ji Asadulmuluuk. Bafade ya ce, yana bayan gari kan wani babban tsauni da babu wani mahaluki da zai iya shiga wurin, a shekarun da suka gabata, lokacin da mahaifin wannan sarauniyar yake mulki, an yi yunkurin kai masa hari don a kore shi ko kashe amma abin ya gagare mu. Allah kadai ya san yawa sadaukan da suka salwanta ta dalilinsa. Dole ce ta sa aka hakura aka kyale shi, yanzu dai muna zaune ne cikin razani, ka ga dai duk wanda zai fita zuwa wani gari ko wata kasa, idan har yana son ya nemi izini to sai ya yanka masa dabba ya kai wani wuri ya ajiye, sannan sai ka zo ka tafi ba tare da fargaba ba, haka zalika idan za ka shigo da bako sai kun taho abin yanka, amma sabanin haka to duk wanda ya zo sai da wani ba shi ba.

Suna cikin haka, sarauniya ta aiko a zo tafi da shi, bayan sun isa wurinta ya yi gaisuwa, sai sarauniya ta ce, ai kun san dokar fitar da shi, yanzu tun da a gidana ya sauka dole ne a fitar da shi ta sahihiyar hanya. Don haka a je inda ake ajiye dabbobinta a dauki bijimin sa, a yanka a kai wa dodo domin ya bari a fita da shi.

Shi dai Asadulmuluuk bai ce komai ba, da aka kammala komai suka yi bankwana da sarauniya ta yi masa goma ta arziki suka fito har bayan gari, daga nan suka ce za su je wurin yanka wannan bijimi, ya je su je tare domin shi ma ya samu ilimin da zai bayar nan gaba.

Ba su yi jayayya da shi ba, suka tafi har wurin da za a yanka wannan bijimin sa, aka yanka a gabansa, ko da jinin ya zuba, sai ya ji wata murya mai gwarji tana cewa, madalla da shigowa da fitar babban bako, madalla da shigowar dan sarki, kai madalla wannan babbar kyauta.

Ana gama fadar haka kawai sai ya nemi wannan bijimi sa da jinin ya rasa wurin ya bushe kamar ba a taba yanka komai a wurin ba, daga nan kuma sai suka juyo suka dawo inda za su yi bankwana, a nan suke gaya masa wannan sa da aka yanka yana daga cikin shanu guda saba’in da biyar da aka yanka saboda baki irinka. “Amma dai kia duka daga inda ka fito kai basarake ne ko?” In ji bafade.

Asadulmuluuk ya ce, bawa dai in dai a ce ni basarake ne ai ba zan zo a wannan yanayi da kake gani ba, amma ina dalilin wannan tambaya? suka ce ai tun da ake yanka shanu ba a taba yankawa talaka ko wani attajiri ba sai basarake, kuma a kalaman dodo ma ya ce madalla da zuwan basarake, wannan ce ta sa muka tambaye ka. Ya yi murmushi ya ce; ” Kawai dai kun riga kun tsorata da shi don haka kuke amincewa da duk abin da ya gaya muku.” Da dai ya ga za su dame shi da tambayoyi sai ya yi sallama da su ya ci gaba da tafiya.

Bayan sun dawo cikin gari suka shaida wa sarauniya, yadda abin ya faru, suke gaya mata mamakinsu da jin yadda sautin dodon ya bayyana shi a matsayin basarake. Sarauniya ta ce, ” Ni ma a daren jiya na yi mafarkai sau uku masu bibiyar juna, cewa shi wannan saurayi basarake ne, kuma na fito ne da niyyar a fita da shi ta inda aka saba fita da wasu mutane sai na ga rashin dacewar hakan gara dai a fita da shi ta hanyar da za ta zama mai inganci domin fadarsa ta cewa daga kasar sarauniya Sa’adiyya yake.

To amma dai ko menene ai mun bashi amana kuma mun bashi kulawa kamar yadda yake a hakkin bako, kuma muna yi masa addu’ar Allah ya kiyaye masa hanya.”

Asadulmuluuk ya cigaba tafiya cikin dajin da sai dai kukan tsuntsaye da sauran kananan dabbobin jeji, har isa garin da zai je, kafin ya isa kan iyaka sai ya hadu da wani bawan Allah ya yi masa sallama ya amsa, ya tambaye wurin da yake nema, mutumnin nan ya nuna masa wani dutse fari mai girma da fadi, ya ce ma ” A kasan dutsen akwai wani Malami yana zaune kan buzu, idan ka je masa sallama ka tambaye shi abin da kake so zai sada da wurin.”

Asadulmuluuk ya yi godiya suka yi bankwana, to wuri ne da ya hango shi daga nesa, a she a kasan dutsen wadansu irin bishiyu manya-manya ma su duhu. Ko da isarsa wurin sai ya ga wurin yana kara yi masa nisa, shi yana zato zai shiga gari, amma ya ga sai shiga jeji yake kara yi, har ya fara tsammanin ko mutumin can ya tura shi inda za a cutar da shi ne, sai kuma ya hango alamar wani gida cikin duhun ganyayen bishiya, sai tunkari wurin ba tare da tsoro ba.

Da zuwa ya samu wannan Malami ya yi masa sallama, Malamin ya amsa masa ya sauko daga dokinsa, Malami ya nuna masa wuri ya zauna, ya fada masa abin da yake tafe da shi, aka ba shi masauki yadda aka ba wa kanwarsa masauki, sannan ya sa aka kawo masa abinci, ya ci ya yi sallar azahar aka nuna masa daki don ya huta zuwa gobe.

Wanda ya raka shi zuwa inda zai kwana ya fada masa cewa, gobe idan Allah ya kaimu za a kai shi wurin da zai yi ziyara da kuma muhallan da zai karbi wasu sakonni daban wadanda za su taimaka masa wajen tafiyar rayuwarsa. Haka zallika an tanadar masa isasshen guzuri na komawawrsa inda ya fito da kuma wasu abubuwa da sai ya je zai ji ko ya gani. Suka yi sallama ya fita.

Exit mobile version