Tare da Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki,
A wannan makon mun zo muku da tattaunawar da muka yi da Wakilin Sarkin Jaba na Zariya da kewaye Mista Yohana Kafarma, kan tarihin wannan kabila ta Jaba, wanda ya kunshi zamantakewarsu da sauran kabilu da tattalin arzikinsu da kuna al’adunsu na gargajiya, wadanda suka hada da auratayya da kuma zamantakewarsu da sauna kabilun da suke tare. Ga dai yadda tattaunawar ta kasance, tare da Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki:
Ranka ya dade masu karatunmu za su so ka gabatar da kanka?
Sunana Yohana Kafarma, ni ne wakilin Sarkin Jaba na Zariya da kewaye.
Tarihin kabilar Jaba yana da tsawo sosai, sai dai mu tsakuro wani abu daga cikinsa,
domin za mu dade muna yi, in na ce zan ba ka tarihin al’ummar, domin kuwa mu Jaba, muna da tarihi kashi-kashi.
In ka ce kana son ka ji tarihi na al’ummar Jaba, zan dan fada maka kadan, domin tarihin na da yawa. al’ummar Jaba suna cikin jihar Kaduna.
Al’ummar Jaba suna zaune a cikin jihar Kaduna, ma fi yawancinsu suna Kudancin Kaduna. Suna zaune da masu karin harshe daban-daban a gurin amma duk Jaba ne. Muna da Karin harshe daban-daban.
Ni mutumin Chori ne, akwai mutumin Nok da Kwai da Dedu da Duya, akwai Bursan, akwai Furze, akwai kuma Fulyom, ga su nan da dama, to a kadan ke nan, in mun ce za mu kira dukkan garuruwan da Jaba ke zaune za mu ga sun kai wajen 50.
Al’ummar Jaba sun zo, kamar yadda idan kana da ‘ya ‘ya da yawa wani ya tashi ya je nan ya zauna ya sake haifar ‘ya’yansa, wancan kuma ya girma kamar yadda mu mun zauna nan Zariya mun haifi ‘ya ‘ya a Zariya, mun yi aure a Zariya, mun haifi ‘ya ‘ya a Zariya wasu ma ba su san ‘ya ‘yanmu a gida ba.
Al’ummar Jaba, babansu ya fara zama a Bauchi, daga Bauchi ya dawo Jos, a Jos ya haifi da daya mai suna Ham, ya zauna a can, yana cikin littafi mai tsarki, sai daya daga cikin ‘ya ‘yan ya zo ya zauna a can wurin mai suna Jaba. Ya bar sauran ‘yan uwan a can.
A cikin zamansan nan, Ham, kana ji a sunan nan ana cewa Ham, to sunannansa ne muka canza, maimakon a ce Jaba da Hausa, sai ana cewa Ham, yana nan a littafi mun gin shi a Bible, ya zo ya zauna a wannan guri sai ya hayayyafa, ya samu al’umma an yadu to cudanyar nan, shi ne ‘ya ‘yan Jaba suka zauna a wurin nan.
Mutanen Jaba mutane ne masu son zaman lafiya da hakuri da masu son neman ilimi, da sana’o’i. Sana’a noman nan, a cikin Jaba to mun zama tsakanin iyaka da Kafancan da Kaciya, rabin Kaciya mutanen Jaba ne.
Duk muke nan tare da Kauru, Kauru kuma an zo an ba su karamar hukuma, ka ga mutanen Jaba tarihinsu kasar Israel suka fito suka yi ta kewayen nan har suka zo nan. Kamar yadda na yi maka bayani kamar ka zo ka zauna nan in ka yi girma ko ka haifi da sai kuma wani ya ce zai je ya ga dan uwansa ya ce, zan je in zauna can.
A hankali sai ya ji dadin zama a wurin sai ya ce ya zauna can. Haka aka yi ta tafiya, halittar Allah ke nan, to shi ne yanzu muna nan wurin a jihar Kaduna, inda za ka ji ana cewa mutanen Jaba.
Bari in dawo bangaren ilimi, mutanen Jabar nan suna addinin Kiristanci sosai a wurin, akwai Masallata akwai wadanda ba su da addini, amma ma fi yawa addi nan nan ne guda biyu, amma ma fi yawa Kirista ne suka fi yawa a wannan wuri a misali ke nan a “population” za a samu wannan, amma in an ce zaman lafiya da cudanya to Jaba yana daya daga cikin sahun gaba.
Inda mutumin Jaba ke aiki, ban ce dukkansu ba, sai ka ji dadin aikinsa. Mutanen Jaba lokacin muna zama ana tsafin nan, addini bai fito ba, sai lokacin da Turawa suka zo yada addini, da suka zo Arewa sun fara sauka a Kano ne, Kano suka kore su, da Kano suka kore su cewa mutanen nan ba wadansu ba, ba sa son wannan, da Kano suka kore su sai suka koma Jos.
Daga Jos kuma sai wasu suka sauka Kagoro, daga Kagoro aka kawo mana addini. Ta yadda addini ya sauka ke nan na Kiristanci har mun samu wani Bature da matarshi har ya samu wani bangare ya zauna. Bangaren Zik muke Kiranshi, aka bude mana asibiti domin an bude makarantu. Haka kuma aka bude asibi domin an bude makarantu su me za ka gani a kasar Jaba.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa.