Connect with us

TARIHI

Asalin Sarautar Katsina, Katsinan Gusau Da Katsinan Maradi

Published

on

A bisa zance mafi shahara an ce, wani mai suna Kumayo ne shugaba na farko a Katsina ko kuma ta na iya yiwuwa shi ne wanda ya kafa garin na Katsina ma kacokam. Sai kuma sarakuna masu suna Ramba, Taryau, Jatinnati da Sanawu su ka biyo bayansa a mulki (tsawon mulkinsu gabadaya kimanin shekaru 350).

An ce, Sanawu ya shafe tsawon shekaru 30 a kan mulkin Katsina, sannan a ka ce Korawa ne su ka kashe shi, wasu al’umma kenan da su ka zo daga ‘Yantandu su ka kafa daular su a Katsina. Su ne su ka damka jagorancin Katsina a hannun Sarki Ibrahim Maji. Watakila hakan ya auku ne a wajejen shekara ta 950 bayan hijira.

Sannan an samu cewa, shekaru 30 kafin zuwan Ibrahim Maji a mulki (wuraren shekarar 1513 miladiyyaa, 919 hijiriyya), dakarun Sarkin Songhay Alhaji Muhammadu Askia sun kwace garuruwan Hausa gabadaya ciki har da Kano da Katsina.

Kamar yadda wasu su ka ruwaito sun ce, lokacin Katsina na karkashin ikon birnin Kano ne kuma garuruwan biyu sun shafe lokaci kalilan ne a karkashin daular ta Songhay, inda daga bisani dukkansu su ka samu ‘yancin kansu.

Amma a hankali sai kasar Katsina ta rika fadada ta na mai lakume kananun masarautu izuwa cikin daularta.

Manyan biranen tsohuwar masarautar Katsina sun hadar da ’Yandoto, Gozaki, Maska, Tasawa, Gazawa, Ingawa, Matazu, Ruma, Kwatarkwashi, Birnin Bakane, Karofi, Maradi, Gwiwa, Kanen Bakashe da suransu. Wannan shi ne kadan daga asalin somawar sarki a birnin Katsina.

Dangane da asalin somawar Sarkin Katsinan Gusau kuwa, shi garin Gusau gari ne da a ka ce an kafa shi a wajajen shekarar 1811 miladiyya bayan saukar wasu mutane daga garin ’Yandoto izuwa wannan wuri.

A na ganin ba komai ya sanya a ke kiran Sarkin Gusau da suna Sarkin Katsinan Gusau ba sai kasancewar a zamanin da Fulani ke jagorancin kasar Hausa har kuma Malam Muhammadu dan Ashafa ya ke jagorancin garin na Gusau, sai Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu ya tsaga kasar Katsina biyu Gabas da Yamma garuruwa saba’in-saba’in ya damka shugabancinsu tsakanin Malam Sambo dan Ashafa da ke zaune a Gusau da kuma Malam Umarun Dallaje da ke zaune a birnin Katsina. Don haka kowannensu sai a ke yi ma sa lakabi da Sarkin Katsina (tunda Katsinan ce a ka raba gida biyu), amma don a rika bambancewa sai a ke kiran Malam Sambo dan Ashafa da sunan Sarkin Katsinan Gusau.

Haka kuma duk sarakunan da su ka biyo bayansa har zuwa yanzu da wancan suna a ke ambaton su.

Haka kuma dangane da asalin sanya wa Sarkin birnin Maradi suna Sarkin Katsinan Maradi, shi ma an samu cewar tun asali Maradawa sun kasance Katsinawa ne ko kuma a ce birnin Maradi asalinsa a karkashin daular Katsina ya ke.

Wasu na ganin cewar yaki ne ya kori Katsinawa daga birninsu su ka je su ka yada zango a Maradi, musamman wuraren da adawa ta yi tsamari tsakaninsu da Gobirawa, amma daga bisani sai wasunsu su ka koma birnin Katsina da zama, saura kuma su ka ci gaba da zama a garin na Maradi har kuma sa’ar da bunkasar garin ya kai ga nada mu su sarki.

Babban abinda tarihi bai manta da shi ba shi ne wanzuwar birnin Maradi a karkashin daular Katsina na tsawon wani lokaci ta yadda daga Katsina a ke nadawa garin sarki. Kuma a kan kira sarkin da suna ‘Sarkin Katsinawan da ke Maradi.

An ce, sai a farkon Karni na 19 ne Maradi ta samu ‘yancin cin gashin kanta, amma kuma har zuwa yanzu ba a daina kiran sarkinta da suna ‘Sarkin Katsinan Maradi’ ba.

Zuwa yanzu birnin ya na cikin Jamhuriyar Nijar ne kuma wata ambaliyar ruwa ce ta sanya mutanen birnin tashi daga ainihin birnin zuwa inda su ke da zama a yanzu a matsayin sabon birnin na Maradi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: