Asalin Wadanda Ba Su Son Hadin Kan Jam’iyyar APC A Zamfara -Sanata Yarima

Jam'iyyar

Daga Hussaini Yero,

Tun bayan da gwamann jiharZamfara   Bello Mattawalle ya koma  jamiyyar APC, wadanda suka dade tare  da shi, su ne wadanda suke ganin ba a yi masu adalci yadda
aka amshe shi hannu biyu a APC ba, yayin da kuma ta bangare daya su ma ‘yan jam’iyyar PDP na yi ma ita jam’iyyar butulci ne.

A kan haka ne shi tsohon gwamnan Jihar Zamfara ,kuma jigo a siyasar Sanata Ahmad Rufai Sani Yariman Bakura ya tabbatar da cewa, wadanda tsohon Gwamna Abdudulaziz Yari Abubukar, ke ma albashi duk wata daga aljihunsa da wadanda shi gwamna Matawalle ya ba mukaman siyasa ne ba su son hadin kan jamiyyar APC a Jihar ta Zamfara.

Sanata Yarima Bakura, ya tabbatar da haka ne a hirar da aka yi da shi a gidan Rediyon Jihar Zamfara.

Yarima Bakura ya kara da cewa, tsohon gwamna Yari a bikin amsar gwamna Matawalle, ya tabbatar da cewa, gwamna Matawalle abokinsa ne, kuma babu wata matsala a tsakanin su, duk kuma wani shedanin da ya ke cikin tafiyar Allah yayi masu maganin sa,wannan ya nuna cewa, babu wata matsala sai dai su magoya bayan sune ke san haifar da matsalar kamar dai yadda Sanata Yarima ya bayyana.

Sanata Yarima ya gargadi magoya bayan su da su ji tsoran Allah su sani cewa,Allah ke azurta mutane ba mutum ba,duk abinda za su samu a rubuce ne yake, idan har ka rasa kujerar Kwamishina ko mai ba gwamna shawara ka dauki abin wata kaddara ce, duk Inda rabonka ya ke sai ka cimmasa.inji Sanata Yarima Bakura.

Daga karshe ya ce kuma da yardar Allah mutane sai sun sha mamaki na ganin yadda Yari da gwamna Matawalle za su hade su zamo tsintsiya daya madaurinki daya.

Exit mobile version