Daga Sadiƙ Tukur Gwarzo
08060869978
Ance wai tun a zamanin da, sa’ar da Sarkin Kano Muhammadu Bugayya ya hau karagar mulkin Kano a shekara ta 1386 bayan mutuwar Sarkin Kano Aliyu Yaji Ɗan Tsamiya aka soma wasan gargajiya tsakanin Kanawa da zage-zage.
Asalin abin akace watarana ne sarkin Kano Bugayya ya fita yaki izuwa ƙasar Zazzau, ya tafi da jarumawan sa masu yawa ya doshi garin Turunku birnin Zazzagawa. Tun kafin ya riski garin sai labari ya iske sarkin Zariya na lokacin Muhammdu Abu cewa ga Kanawa nan suna zuwa Zazzau da yaƙi.
Lokacin da Kanawa suka iso, tun daga nesa suka hango dakarun Zazzau a saman dutse, don haka kai tsaye sai suka tunkari gindin dutsen, sai jiyo mai shela akayi acikinsu yana shelanta cewa duk mutumin Kano ya naɗa gammo, zamu taru mu ɗauki dutsen kufaina tare da mutanen da ke kansa mu tafi dasu Kano da sauri. Daga nan sai kurum akaji Kanawa sun ɗauki sowa suna faɗin hoɗɗasa! Hoɗɗasa! Hoɗɗasa!
A ka ce dajin haka sai Sarkin Zazzau Muhammadu Abu yace ga mayakansa “Yaku jaruman Zazzau, kada kowa ya motsa, wannan zambo ne na Kanawa ɓarayi mazambata. Ko aljanu basu iya daukan dutsen nan in ba mala’iku ba”.
Kunsan Zazzagawa (ga tsoro, kuma ba wayau), sai sukaki jin umarnin sarkin su. Suka rinka tsalle daga can kololuwar dutse suna tumowa kasan dutse, jikake TIM. Wasu suka faɗo matattu, wasu kuma suka faɗo karyayyu, wadansu kuma basu karye ba amma dai sun suma. Kanawa na ganin haka sai suka tattara sumammun da karyayyun sukayi awon gaba dasu izuwa Kano, akabar matattu yashe a gindin dutse, acan aka maishe su bayi bayan sun murmure.
A can birnin Turunku kuwa, bayan Kanawa sun janye jikinsu daga ƙasar Zazzau, sai Sarki Muhammadu Abu ya tarasu, yayi musu faɗa da gargaɗi a kan kin bin umarninsa da sukayi. Yake cewa ku Zazzagawa kun bani kunya, me yasa kuka ki jin magana ta kukayi ta tsalle kuna faɗowa gaban Kanawa mazambata?
A nan ne sai wasu daga mayakan Zazzagawa suke cewa Ran sarki ya daɗe, yayin da mukaji Kanawa na fadin hoɗɗasa, sai mukaji tamkar sun daga dutsen, suna tafiya dashi izuwa Kano. Mu kuma sai mukayi ta tsalle don ba ma so Kanawa su tafi damu Kano. Sai sarki yace wannan ai zambo ne irin na barayi.
An ce tun daga wancan lokaci aka samo wasan gargajiya wanda akeyi tsakanin Kanawa da zage-zage.
Marubuci Maje Ahmad Gwangwazo (Allah yajikansa da rahama) ya ruwaito kwatankwacin haka a littafinsa ‘ Tarihin Kano kafin zuwan Jihadi: Wangarawa sun iso Kano. Littafi na biyu. Amma kuma Zazzagawa sun musanta hakan inda sukace wasan ya samo asali ne alokacin da Gimbiya Amina ta Zazzau taci dakarun Kano da yaki, ta korasu har cikin birninsu a fusace. Don haka bayan an yi sulhu, sai tsokana ta rinka shiga tsakani. Shine kuma har yau ake wannan wasa.