Asarar Da Aka Tafka Sakamakon Banka Wa Ofishin INEC Wuta A Akwa Ibom  

Ofishin INEC

 

Daga Khalid Idris Doya,

A jiya ne wasu wadanda ba a san ko su waye ba suka banka wuta wa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke karamar hukumar Essien a Jihar Akwa Ibom wuta.

 

Babban Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin yada labarai da wayar da kai, Festus Okoye ya tabbatar da faruwar wannan lamarin a sanarwar da ya fitar wa ‘yan jarida a jiya, ya kuma ce wannan lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi 2 ga watan Mayun 2021.

 

Wani bangare na sanarwar na cewa: ‘Kwamishinan hukumar zabe na Jihar Akwa Ibom Barista Mike Igini ya tabbatar mana da cewa ofishinmu da ke karamar hukumar Essien Udim ya kamata da wuta sosai.

“Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi. Jami’an tsaron mu da suke bakin aiki babu wanda ya ji rauni amma gine-ginenmu da kadarorinmu sun lalace sosai. Mun tafka mummunan asarar sakamakon wannan gobara da aka kunna.”

Daga asarar da aka tafka kuwa, ya ce “Ababen da suka salwanta yayin wannan wutar da aka kunna sun hada da akwatinan jefa kuri’a 345, kananan kuri’u 135, wayoyin aiki, tankokin ruwa, kujerun zama da na ofis tare da sauran muhimman Kayayyakin mu.

“Jami’an tsaron ‘yan sanda sun kaddamar da fara bincike kan faruwar wannan lamarin. Harin baya-bayan nan da aka kaddamar kan cibiyoyinmu tattare da cewa mun rigaya mun fara adana kayan zaben 2023 a sassan kasar nan abun damuwa ne matuka.”

Hukumar ta gargadi masu kai hare-haren muhallanta da cewa ba za su samu nasarar kawo mata jinkiri a shirye-shiryenta kan zaben 2023 ba kuma ba za su taba cimma nasara ba.

“Idan ba a magance irin wadannan hare-haren ba zai zama nakasu ga hukumar nan a shirye-shiryenta na cigaba da aikin rijistan masu neman mallakar shaidar katin yin zabe.”

Hukumar dai ta sha alwashin cigaba da yin aiyukanta yadda ta tsara har ma a Jihar Akwa Ibom domin tabbatar da komai ya tafi mata yadda ake so.

Exit mobile version