CRI Hausa
Asilihan Nazha’erhan mai shekaru 56, dan asalin kabilar Kazakh ne dake zaune a jihar Xinjiang ta kasar Sin. Cikin shekaru 25 da suka wuce, shi ne limanin Masallacin dake garin Hongdun na birnin Altay dake jihar Xinjiang.
An gina masallacin garin Hongdun a shekarar 1996, kuma a yanzu a ko wace rana, akwai mutane kimanin dari 1 da suke yin sallah sau biyar a wannan masallaci. A ranar Jumma’a kuma, mutane kimanin dari 2 suna zuwa masallacin, dukkansu su mutane ne dake zaune kusa da masallacin garin na Hongdun.
Asilihan Nazha’erhan ya ce, “a kan gayyace ni na jagoranci bikin aure a lokacin da mutanen wurin suka aure. Haka kuma, na kan jagoranci jana’izar mamata bisa ka’idar addinin Musulunci. A jihar Xinjiang, gwamnatin na kiyaye dukkanin ibadun addinin Musulunci bisa dokoki, kuma, ana girmama al’adun addinin Musulunci kamar yadda ake fata.
A ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2021, Asilihan Nazha’erhan ya halarci taron manema labarai, game da harkokin dake shafar jihar Xinjiang, wanda ofishin watsa labarai na gwamnatin yankin Xinjiang mai cin gashin kansa na kasar Sin ya kira.
A yayin dake tsokaci game da jita-jitar da wasu kafofin watsa labaran kasashen ketare suke yadawa cewar, wai kasar Sin na hana ‘yancin bin addini a jihar Xinjiang, Asilihan Nazha’erhan ya ce, “karya ce suka fadi, domin cimma mugun burinsu na lalata hulda mai kyau, dake tsakaninmu da gwamnatin kasa, da kuma kawo sabani a tsakanin Musulmai da wadanda ba sa bin addinin Musulunci, domin halaka zaman rayuwarmu baki daya, amma ba za mu saurari karairayin su ba, kuma, ba za su cimma mugun burinsu ba!” (Mai Fassarawa: Maryam Yang)