Daga Idris Umar, Zariya
Ranar Litinin din da ta gabata ne dubun wasu gungun barayi ta cika a harabar Jami’ar Ahmadu Bello da ke Samarun Zariya.
Wakilinmu ya sami leka wa cikin Jami’ar don gane wa idonsa yadda lamarin ya faru da har barayin suka shiga hannun jami’an tsaron Jami’ar.
A ranar, harabar Jami’ar cike take da dalibai daga ko’ina a fadin kasar nan don zana jarabawar tantancewar shiga Jami’ar, don haka duk wanda ka gani za ka ga kansa a duke yake ba abin da yake tunani sai abin da zai zana wajen jarabawarsa, wasu kuma iyaye ne sun kawo yaransu don su sami damar zana jarabawar, don haka kowa ka gani cikin hanzari yake.
Ana cikin wannan yanayi sai wani ma’aikacin F.C.E Zariya, Umar Isa, ya je First Bank da ke PZ Zariya don ya cire kudinsa ashe duk abin da yake yi yana yi ne a kan idanun wadannan barayi. Sai da suka bari ya karbi kudin naira dubu dari biyu ya fito da su a leda ya shiga motarsa kirar Honda mai lamba AA386 NTT ya nufo garin Samaru yana zuwa Samaru sai ya shiga ABU don gudanar da wasu harkoki nasa, to mai zai faru nan ne wakilin namu ya yi wa daya daga cikin barayin tambaya ko me ya faru daga a nan ?
Sai Nuhu Garba, daya daga cikin barayin kuma dan kimamin shekara 40 da haihuwa ya ce, “wallahi tun daga Kaduna nake kuma kungiyace mu ke da ita kuma muna da yawa ko a yau kusan mota biyu muka shigo don gabatar da wannan mumunar sana’ar tamu don haka ne ma mu kai ta bin wannan mutumin tun da ya fito daga banki har zuwa cikin ABU kuma yana tsaya wa muma muka sami wani waje muka dakata sai da ya fita sai muk ayi amfani da ta mu basirar muka fasa motar muka kwashe kudin da ya karbo. Da yake dubu ta cika nan take mutane suka farga mu ne muka fasa wannan motar sai aka ce da wa Allah ya hada su? in bada mu ba, mu kuma gashi ba mu san hanyar Jami’ar ba sosai ba hakan ya sa muka danno hanyar da take a kulle sai kawai jama’ar da ke wajen suka taimaka aka kama mu. Gashi mun zo hannu ka ji yadda lamarin ya faru”
Nuhu Garba dai a Kaduna yake da zama kuma yana aiki ne da wani garejin walda da ke kera kofofin karfe na zamani da ke kawo Kaduna kuma ya shaida wa wakiln LEADERSHIP A YAU cewa, tabbas babu wanda ya san yana wannan sana’ar ta fasa mota da kwashe kayan da suka samu a cikin ta,sai ‘yan kungiyarmu, kuma a kalla ya shekara 3 da fara sana’ar tasu, amma ya zuwa lokacin kamun nasu sun fasa a kalla motoci sun kai 5 kuma da Naira dubu dari da hamsin ya fara satar( 150,000) sai kuma dubu dari Uku (300,000) sai kuma dubu dari ( 100,000) dadai sauran su, kuma ya ce a gaskiya shi ba barowo ba ne a lokutan baya amma shi wannan wanda aka kamasu da shi mai suna Alhaji Ibrahim Musa to shi ya koya masa satar a lokacin da yake zuwa sayan kofofi a garejin su da ke kawo Kaduna.
Shi ma Alhaji Ibrahi Musa dan shekara 70 wanda yake zaune a jihar Kano a wata Unguwa mai suna Rimin-kebi kuma yana da yara da mata, shi ma bai musu daga abin da aka kamasu akai ba inda ya ce, “Tabbas mun biyo wani ne daga banki muka fasa motarsa muka kwashe kudinsa amma sai gashi an kamamu” .
Amma bincike ya nuna cewa, barayin na da mambobi masu yawa a yankin Zariy,a kuma sukan amfani ne da lokutan da ake gudanar da taro ko kuma karshen wata don masu karbar albashi.
Bugu da kari, su barayin, sukan yi shigar kece raini ne yayin da suka fito sana’ar tasu ta fasa motocin jama’a kuma ba sa zuwa da karamar mota sai babba mai tsadar gaske kuma a kungiyar nasu sukan hada da tsoffi don basaja a yayin da rana ta ba ci, in an biyo su a kan titi za ka ga yaro da tsoho a motarsu kai ka ce uba da dansa ne za su unguwa a cikin motar amma ina tsahon mugu ne.
Hakan yasa ma wakilin LEADERSHIP A YAU ya waiwayi shi tsohon barawon da tambaya kamar haka, ko akwai kira da zai yi wa masu irin sana’a irin ta su ta zuwa bakin banki a tsaya in an ga wani ya zo ya karbi kudi sai a bi shi a fasa masa mota a kwashe masa kudin? Sai ko ya ce, “ Su ji tsoran Allah su bari don ba sana’a ba ce tagari, muma muna rokon Allah yasa ita ce ta karshe a gare mu”.
Shi ma Nuhu cewa, ya yi “A gaskiya nayi nadamar rungumar wannan sana’ar da na yi gashi ta kaini ga mawuyacin hali amma in Allah yaso wannan itace karshe don zan koma wajan aikina na walda su kuma sauran abokan satar tamu to don Allah ina kiran su da su bar sata sumu koma ga Allah.
Kanar Jibril Tukur, mai ritaya shi ne shugaban sashin tsaro na jami’ar ta Ahmadu Bello Zariya ya yayin da yake wa wakilin LEADERSHIP A yau Karin harske akan nasaran da yaransa suka samu na cafke wadacan barayi sai ya ce ,“ Wannan dole ne mu gode wa Allah bisa ga kariya da Allah ya yi wa hukumar tsaron ta jami’a baki daya ,kuma nayi jinjina ga dukkan jami’an tsaron jami’ar Ahmadu Bello baki daya bisa ga kwarewarsu a fagen aikin tsaro, kuma a shirye muke mu ci gaba da kare rayukan mutanen da muke tare da su da dukiyoyin su don kaha muna son a ci gaba da bamu hadin kai kuma mutane su kiyaye da duk wata doka da aka tsara don hakan ne kan sa mukan gane bata gari kuma zamu dukufa wajan binciken tsarin da zai sa jama’ar da ke jama’ar ABU sun sami kwanciyar hankali a ta bangaren tsaro baki daya.
Jama’a ne da yawa suke ta godiya da jinjina ga hukumar tsaraon jami’ar bisa ga yadda suka kama barayin ya gudana cikin tsafta da ilmi domin barayin sun dade suna addabar mutane a lokutan baya, domin babu dama, ka ajiye motarka ka tafi ka dawo sai ka tarar an sace ta.
Ya zuwa hada wannan labarin barayin na hannun sashin tsaro na hukumar jami’ar don ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da su a gaban kuliya.