Asirin Kwalejojin Ilimi 41 Da Ke Ba Da Shaidar NCE Ta Bogi Ya Tonu A Bauchi
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asirin Kwalejojin Ilimi 41 Da Ke Ba Da Shaidar NCE Ta Bogi Ya Tonu A Bauchi

byKhalid Idris Doya
3 years ago
Ilimi

Hukumar kula da Kwalejojin Ilimi a Nijeriya (NCCE) ta rufe tare da kulle cibiyoyin ilimi guda 41 da ke bada shaidar karatun ilimi ta NCE na bogi a jihar Bauchi.

A wata wasika da hukumar ta aike wa kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Dakta Aliyu Usman Tilde mai dauke da kwanan wata 5 ga watan Satumba 2022 da wakilinmu ya ci karo da ita a ranar Laraba, na cewa dukkanin cibiyoyin ilimi da Kwalejojin ilimi da lamarin ya shafa an basu wata daya tak da su tabbatar sun kulle ko kuma su fuskanci shari’a.

  • Kotun Daukaka Kara Ta Umurci Kungiyar ASUU Da Ta Gaggauta Janye Yajin Aikin Da Take
  • Yaya Ake Gane Alamomin Mutum Ya Yi Kyakykyawan Karshe?

Wasikar wacce babban sakataren hukumar mai cikakken iko, Farfesa Paulinus Chijioke Okwelle ya sanya wa hannu, ya yi tilawar cewa a watan Oktoba da Nuwamban 2021 hukumar ta gudanar da wani atisayen zagayen kwalejoji a fadin kasar nan domin bankado makarantun da ke bada shaidar kamala karatun NCE na bogi, inda a bias hadin kai jihohi suka basu aka samu nasarar gudanar da aikin binciken cikin nasara.

A cewar hukumar NCCE an tura wa ma’aikatar ilimi ta tarayya rahoton aikin binciken da aka gudanar sannan kuma aka bai wa hukumar umarninta gaggauta kulle dukkanin cibiyoyin da ta gano na bogi ne.

“Kan wannan, hukumar nan tana jawo hankalin Gwamnatin jihar Bauchi da ta taimaka mana wajen tabbatar da wadannan makarantun sun kasance a kulle da suke bayar da shaidar NCE na bogi,”Okwelle ya kara.

NCCE ta jero sunan kwalejoji da cibiyoyin ilimin da wannan kullewar ta shafa da aka gano suna gudanuwa ta haramtacciyar hanya da cewa sune kwalejin ilimi Mayo Belwad a ke hadin guiwa da kwalejin ilimi ta Azare; kwalejin ilimita Abubakar Adamu Mu’azu da ke Boto; Al-Iman College of Education, Nasarawa. Nasarawa, Bauchi, da kwalejin ilimi ta Aped da ke Liman Katagun, Bauchi. Sauran sun kunshi kwalejin ilimi da ke Bununu a karamar hukumar Tafawa Balewa; kwalejin ilimi mai zurfi da ke Magama, Gumau, Toro; kwalejinkoyar da ilimin larabci da addini da ke Toro; kwalejin SACH da ke Bauchi, makarantar koyar da ilimin Kimiyyar lafiyar muhalli (EHS) da ke Bauchi; kwalejin ilimi ta ECWA da ke Bayarw da kuma cibiyar ilimi ta Garba Ibrahim.

Cibiyoyin ilimin da rufewarta shafa har da cibiyar koyar da ilimin addini da larabci ta Murkazul Islam da ke Azare; Azare Sahib Collegeof Education; kwalejin ilimi ta Sardauna da ke Bauchi; kwalejin ilimi ta Sheikh Adamu Abubakar da ke Azare; Sunnah Bauchi College of Education, Toro; Thomas Moor Institute, Bauchi; Urat Memorial Collegeof Education, Bauchi; Diamond Teachers Training College ofEducation, Bauchi da kuma kwalejin ilimi ta Ibrahim Bello da ke Magama Gumau.

Sauran sun hada da kwalejin ilimin addini da larabci ta Annur Kano da ke Bauchi; kwalejin ilimin addini da larabci ta Annur Kano da ke karamar hukumar Katagum; kwalejin ilimi da ke Burra Ningi; Annur Kano College of Education, Giade; kwalejin Sheikh Adam, Azare, Bauchi; Annur Kano College of Education da ke karamar hukumar Warji; Da’awa Bauchi College of Education, Darazo; Da’awa Bauchi College of Education, Kafin Kafin Madaki, Bauchi; Danyaya College of Education, Miya Ganjuwa Miya Ganjuwa LGA, Bauchi; Darazo College of Education, Akuyam; Gindiri College of Education, Warji LGA, da kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi Kumbotso Gidan Marayu Katagum Zaki.

Farfesa Okwelle, “Dangane da wannan matakin, kwalejoji da cibiyoyin da lamarin nan ya shafa suna da zarafin wata daya da su kulle ko su fuskanci shari’a.”

LEADERSHIP Hausa ta yi tilawar cewa a watan Yuli 2021 Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta nuna damuwarta kan cibiyoyin da aka gano suna ba da shaidar kammala karatun NCE na bogi a jihar. A kudirin da mambar Majalisar mai wakiltar mazabar Hardawa, Hon. Mohammed Babayo ya gabatar, ya ce wannan lamarin na shafan harkar ilimi a jihar tare da gurbata sashin ilimi.

A cewarsa, cikin kwalejin ilimi masu zaman kansu guda 58 da ke ba da shaidar kammala NCE, guda 13 ne kacal suke da rijista da NCCE.

Majalisar ta bukaci Gwamnatin jihar Bauchi da ta tuntubi hukumar NCCE da hukumar NBTE domin lalubo bakin zaren dakile makarantun da suke ba da shaidar NCE na bogi a jihar.

A cewarsa, “Akwai bukatar cikin gaggawa a shawo kan wannan matsalar domin tsarkake harkokin ilimi.”Nan take, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Abubakar Y Sulaiman ya umarci kwamitin Majalisar na ilimi da ya bincike lamarin sannan ya gabatar musu da rahoto cikin kwanaki 30.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya
Manyan Labarai

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace
Labarai

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Next Post
Kasar Sin Ta Mika Dakin Adana Magunguna Na Zamani Ga Zimbabwe

Kasar Sin Ta Mika Dakin Adana Magunguna Na Zamani Ga Zimbabwe

LABARAI MASU NASABA

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version