Khalid Idris Doya" />

Asiya Ganduje Ce Ta Lashe Gasar NNPC Bana

A ranar Larabar da ta gabata ne diyar gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, ta samu gagarumar nasarar lashe gasar da kamfanin Mai na kasa (NNPC) ta shirya, inda ta amshi lambar yabonta a kan hakan.

Gasar wacce ta karade masu so shiga a fafata da su daga sassan kasar nan a tsakanin maza da mata dattijai da matasa da matsakaita na kamfanin, cikin ludufin Allah ita ce ta samu lashe gasar gaba daya.

Cikin gasar ta (HSE COMPETITION) ta makon shekarar 2019, duk da kasancewar Hajiya Asiya a matsayin wacce ta fi kowa karamin shekaru a cikin wadanda suka shiga gasar, samun nasarar nata ya daukaka lifafarta gaya lura da wadanda ta kara da su a gasar.

Shugaban rukunin kamfanin (NNPC) Mele Kolo Kyari, wanda ya samu wakilcin babban jami’in gudanarwa na hukumar, Malam Farouk Sa’id, ya mika wa Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje lambar yabon a madadin kamfanin gaba daya saboda wannan gagarumar nasara da ta samu.

NNPC ta tayata murnar lashe gasar na wannan shekarar.

A babgarenta, Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje (Fulani Zanan Laisu Fika) ta nuna gayar farin cikinta da murnar samun wannan gagarumar lambar yabon a bisa kwazonta, sai ta yi fatan samun karin nasarori a nan gaba, kana ta kuma yaba wa hukumar NNPC a bisa karramata da suka yi da wannan lambar yabon.

Da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan nasarar, Shugaban Kamfanin Dokin Karfe Consultancy Serbices Nigerian LTD,  Bashir Abdullahi El-bash ya bayyana cewar suna cike da farin ciki, “hakika wannan abin alfahari ne ga al’ummar jihar Kano gaba daya, duba da yadda diyar mai girma gwamna ta samu wannan nasara a matakin kasa gaba daya. Kuma duba da kaifin basira da hazaka da jajircewa irin na Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje (Fulani Zanan Laisu Fika) ko shakka babu fiye da wannan nasara ma za ta iya samu,” A fadin shi.

El-bash ya kara da cewa, “dumbin al’umma a wannan jihar Kano sun taya Hajiya Asiya Balaraba Abdullahi Ganduje, murnar wannan nasara da ta samu. Tare da yi mata fatan Allah ya kara mata nasara a rayuwa, gami kuma da fatan daukaka ga gwamna Ganduje,” A fadin shi.

Fasihi a harkar yanar gizo-gizo, El-Bash ya kuma bayyana cewar Asiya Ganduje ta kasance hazika mai kokarin taimaka wa al’umma, don haka ne suka yi farin ciki da samun nasarar nata.

Exit mobile version