Husaini Baba" />

Asmau Habibu Ta Zama Gwamnar Zamfara Na Tsawon Mintina 15

Karon farko yarinya ‘yar shekaru 13 mai suna Asmau Habibu ta zama gwamnar jihar Zamfara na tsawon mintuna 15 kacal.

Gwamnan jihar, Hon. Bello Muhammad Matawalen Maradun, ne ya mika wa Asmau, wacce daliba ce a makarantar Model Primary da ke Tsafe, aikin jan ragamar tafiyar da mulkin gwamnatin jihar na tsawon mintunan a matsayin rikon kwarya, saboda nuna farainsa ga Ranar ’Ya’ya Mata ta Duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a duk ranar 11 ga Oktoba na kowacce shekara, domin gudanar da bukukuwa, inda a bana UNICEF ta yi wa ranar take da G4G.

Jim kadan da amsar mulkin, Gwamna Asmau Habibu ta bayar da umarnin cigaba da inganta tsaro da kuma kara wa jami’an tsaro kwarin gwiwar samar da shi da kuma bunkasa ilimin ‘ya’yan mata da cigaban ilimi bakidaya a jihar.

Cikar wa’adin Gwamna Asamau ke da wuya, sai ta dawo wa da Gwamna Bello Matawalen ragamar mulkin jihar nan take.

Gwamna Matawalen Maradun ya jinjina ma tsohuwar gwamnar mintuna 15, kuma ya yaba da kakarinta wajen kaddamar da kudirin cigaban jihar a tsawon wa’adin mulkin nata.

Gwamna Matawallen ya kuma dau alwashin dorawa daga inda ta tsaya ta fuskar bunkasa rayuwar mata da ganin sun samu ingantacen ilimi zamani da na addini.

A nata jawabin, matar gwamnan jihar, Hajiya Aisha Bello Muhammad Matawalle, ita ma ta bayyana kudirinta na bunkasa Iilimin ‘ya’ya mata da kuma ganin sun zamo hazikai wajen iya harshen Larabci da Turanci.

Kuma ta jinjina wa Gwamna Matawallen Maradun kan kakarinsa na bunkasa ilimin, wanda yanzu haka ya bada ayyuka a hukumar bada ilimi baidaya na sama da biliyan biyar, don cigaban Ilimi a matakin farko.

Wadanda su ka shaidi wannan bada mulkin a gidan gwamnatin sun hada da Shugaban Ma’aikata na jihar Zamfara, Alhaji Kabiru Dan Isa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Bala Bello Maru, da babban sakataren gidan gwamnatin, Alhaji Ibrahim Kaura.

Exit mobile version