Asusun CFRD Na Kasar Sin Ya Amsa Sunansa
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Asusun CFRD Na Kasar Sin Ya Amsa Sunansa

byCMG Hausa
3 years ago
CFRD

Galibi ana kafa asusu ne da nufin inganta fannoni na ilimi ko harkokin ci gaban mata da kananan yara ko raya harkar lafiya da agazawa wadanda bala’o’i suka shafa da makamantansu.

Kamar sauran irin wadannan asusu da kasashe ko al’ummomi ko kungiyoyi masu zaman kansu ke kafawa, shi ma asusun raya yankunan karkara na kasar Sin ko CFRD a takaice, ya amsa manufofin kafa shi, duba da irin managartan ayyukan da yake gudanarwa a ciki da wajen kasar.

  • Magance Tashin Hankali Mai Nasaba Da Harbin Bindiga Shi Ne Ma’aunin Demokiradiyar Amurka

Ayyuka na baya-bayan da asusun ya gudanar a kasar Habasha, ya samu yabo da jinjina, a daidai lokacin da aka yi bikin cikarsa shekaru 3 da bude ofishinsa a kasar ta Habasha.

Shi dai asusun ya fara gudanar da ayyuka daban daban a Habasha tun daga shekarar 2015, an kuma yi masa rajistar gudanar da ayyuka a matsayin asusun ba da tallafin jin kai na kasa da kasa a kasar a watan Yulin shekarar 2019, inda ya karkata ga zurfafa hadin gwiwar musaya tsakanin al’ummun Sin da na kasar Habasha.

Bayanai na nuna cewa, asusun CFRD ya shafe shekaru 7 yana gudanar da ayyuka daban daban a Habasha, ciki har da ciyar da daliban makarantu, da raba kayan karatu, da kayan abinci, da ruwan sha da ayyukan tsaftar muhalli, da ayyukan bunkasa tattalin arzikin mata, ayyukan da suka amfani sama da ’yan kasar Habashan 250,000.

Hakika ayyukan asusun CFRD, sun yi daidai da muhimman ayyukan da gwamnati da al’ummun Habasha ke bukata, wadanda ke da matukar tasiri ga ci gaban kasar.

Sabanin yadda wasu kasashen yammacin duniya ke kafa asusu da sunan raya demokiradiya ko Ilimi ko wasu bangarori na rayuwa, amma suke fakewa da hakan wajen tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe da ma neman shafa musu bakin fenti ko hana ci gabansu.

Wannan ne ma ya sa babban daraktan kungiyoyi masu zaman kansu na kasar Habasha Jima Dilboi ya yi kira ga asusun na CFRD, da ya jagoranci kungiyoyi masu zaman kansu dake Habasha, wajen kulla alaka da sauran kungiyoyi da hukumomi na kasa da kasa, kamar shirin samar da ci gaba na kasa da kasa, da na hadin gwiwar bunkasa kasashe masu tasowa, da shirin ziri daya da hanya daya. A daina fakewa da guzuma ana harbin karsana. (Ibrahim Yaya)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa
Daga Birnin Sin

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Next Post
Kwastam Ta Kama Katan 1,700 Na Jabun Tumatirin Gwangwani A Tashar Ruwa Ta Legas

Kwastam Ta Kama Katan 1,700 Na Jabun Tumatirin Gwangwani A Tashar Ruwa Ta Legas

LABARAI MASU NASABA

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version