Akalla sama da Matasa 300 ne za su ci gajiyar tallafi daga asusun hukumar horar da Matasa sana’oi domin dogaro da kai, ITF, da ke Kaduna.
Manajan shiyya na ITF da ke Jihar Kaduna, Alhaji Yahaya Manu, shi ya sanar da hakan yayin da Shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Kaduna, su ka kai ma sa ziyara a ofishinsa da ke Kaduna.
Ya ce, kungiyar ‘yan jaridar Jihar Kaduna su ma za su amfana da shirin asusun, domin ganin sun bunkasa rayuwarsu baya ga aikin jarida.
Alhaji Yahaya Manu ya bukaci kungiyar ‘yan jaridar da ta dauki matakan da su ka kamata domin dakile ‘yan jarida na bogi, ya na mai cewa, “duk lokacin da mu ka shirya taro za ka ga ‘yan jarida guda 30 zuwa 40 wanda wasunsu ba mu gayyace su ba, amma da zarar ka tambaye su wurin da su ke aiki, sai su fada ma ka sunan wata kafar yada labaran da babu ita.
“Saboda haka ya kamata ku dauki matakan da su ka kamata wajen magance matsalar ‘yan jaridar bogi.”
A nasa jawabin, shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, Kwamared Adamu Yusuf, ya bayyana gamsuwarsa a kan yadda asusun na ITF ya ke gudanar da aikinsu.
Kwamred Adamu Yusuf ya bayar da tabbacin cewa kungiyar NUJ za ta yi aiki kafada da kafada da Asusun domin cigaban ‘yan jaridun.
Shugaban kungiyar ‘yan jaridun ya ce, NUJ za ta yi bakin kkarinta wajen tsabtace aikin jarida a Jihar Kaduna, da a daukacin kasar bakidaya.